Aikin Hajji: Fiye da rabi na maniyyatan Jigawa ba za su je aikin Hajjin bana ba

Aikin Hajji: Fiye da rabi na maniyyatan Jigawa ba za su je aikin Hajjin bana ba

Binciken hukumar Alhazai ta jihar Jigawa ya bayyana cewa fiye da rabin mahajjatan jihar ba za su samu damar aikata hajjin na bana ba sanadiyar tsadar kudin kejerar ta bana.

Alamu sun bayyana cewa fiye da rabin maniyyatan jihar Jigawa ba za su samu damar gudanar da aikin Hajjin bana sanadiyar gazawar da suka yi wajen bayar da cikon kudin kujerunsu bayan da aka kayyade kudin kujerar Naira miliyan daya da rabi.

Bincike ya nuna cewa fiye da rabin maniyyatan ba za su samu damar gudanar da aikin Hajjin na bana ba saboda tsadar da kujerar ta yi a wannan shekara.

Kakakin hukumar Alhazai ta jihar Jigawa, Malam Ibrahim Saalisu Kanya, ya bayyana cewa Hukumar gudanar da harkokin Alhazai ta kasa ta kebewa jihar Jigawa kujeru 2,677, amma har zuwa lokacin da aka fara tashin Alhazai na kasar nan maniyyatan da suka bayar da cikon kudadensu na kujerun ba su wuci 1,412.

Aikin Hajji: Fiye da rabi na maniyyatan Jigawa ba za su je aikin Hajjin bana ba
Aikin Hajji: Fiye da rabi na maniyyatan Jigawa ba za su je aikin Hajjin bana ba

Kakakin hukumar ya bayyana cewa hukumar Alhazai ta jihar za ta mayarwa da Hukumar ta kasa sauran kujerun da maniyyatan na Jigawa su ka gaza bayar da cikon su don ta sayarwa da mabukata kujerun.

Shi kuwa sakataren hukumar Alhazai na jihar Jigawa, Alhaji Sani Muhammed Alhassan, ya ce jihar Jigawa ce tafi kowa ce jiha arhar kujerun bana saboda an samu ragin Naira dubu 100 a kan sauran jihohin kasar nan.

KU KARANTA: Kiwon Lafiya: Nau'ikan abinci 3 da su ke rage nauyin jiki

Rahotannin su bayyana cewa gwamnatocin baya sun rika saye sauran kujerun da jihar ba ta siyar don su rabewa ma'aikatan ta tare da cikawa wadanda suka gaza bayar da cikon kudadensu don su samu sauke farali a kasa mai tsarki.

Mallam Kanya ya ce ana sa ran a ranar 17 ga watan Agustan nan ne maniyyatan jihar za su fara tashi zuwa kasa mai tsarkki kuma wasu suna ganin cewa gwamnatin jihar karkashin gwamna Muhammadu Badaru Abubakar za ta saye sauran kujerun ko wasu daga ciki don ta rabewa ma'aikatan ta don taimakon al'ummar jihar.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel