Wakar cin mutuncin Igbo: Ku daina tsokanan Ibo - Orji Kalu yayi gargadi

Wakar cin mutuncin Igbo: Ku daina tsokanan Ibo - Orji Kalu yayi gargadi

-Bambanci addini da na kabilanci yakamata ya kawo ma Najeriya cigaba

-Hadin kan Najeriya ya zama dole

- Kabilan Ibo ba za su mai da martani akan wakan cin mutuncin da aka musu ba

Tsohon gwamnan jihar Abia, Dr Orji Uzo Kalu, ya nuna bacin ransa akan wakar da akayi na zagin kabilan Ibo wanda yake ta yawo a cikin kasa.

Babban dan siyasa kuma shahararen dan kasuwa, Dr.Kalu yakara dace wa bambanci addini da na kabilanci yakamata ya kawo ma Najeriya cigaba ne, ba ci baya ba. Saboda haka yakamata a dauki matakan hana ire-iren wannan wakokin.

Ya caccaki masu daukan nauyin wakokin cin mutunci, ya kuma kara da cewa “Najeriya ya zama daya babu wanda zai iya raban kan al’umman ta.

Wakar cin mutuncin Ibo:Ku daina tsokanan Ibo-Orji Kalu yayi gargadi
Wakar cin mutuncin Ibo:Ku daina tsokanan Ibo-Orji Kalu yayi gargadi

Ya ce: “Wakan cin mutunci Ibo da aka yi, anyi shi ne domin a fusatar da yan kabilan, amma kabilan Ibo baza su mayar da martani ba, mutane ne masu san zaman lafiya da bin doka. Zamu kiyaye duk wani abu da zai jawo rikici a Najeriya

KU KARANTA:Jonathan yayi Magana aka kisan da aka yi a Ozubulu, da kuma wakan batanci da aka yiwa kabilan Ibo

Najeriya kasa ce da ta kunshi kabilu daban-daban, kuma babu wata kabila da zata ce ita kadai c eke da kasan. Dukan mu masu rikon amana ne, ko kai Bayarabe ne, Ibo, Hausa, Tiv, Efik ko Ijaw da sauran su.

Ibo za su cigaba da ba da gudumawan si dan cigaban Najeriya, ta fannin kasuwanci, da sauran su duk da tsokanar da ake musu.

Tsohon gwamnan yace hadin kan Najeriya yazama dole akan su

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ka ji inda ake da matsala a Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel