Wata kungiyar Neja Delta ta sake bada wa'adin abar musu yankinsu a watan Oktoba

Wata kungiyar Neja Delta ta sake bada wa'adin abar musu yankinsu a watan Oktoba

- Wata kungiyar Neja-Delta tace ‘yan arewa da kabilar yarabawa da suke Niger Delta su bar musu yankinsu kafin kamawar watan Oktoba

-Suna kira da gwamnatin tarayya ta basu ikon mallakar arzikinsu gabadaya

- Bayan kungiyar samarin arewa ta ce kabilun Ibo su bar mata yankinta, 'yan Neja Delta sun bukaci 'yan arewa su tattara daga nasu yankin kafin Oktoba

Wata kungiyar Neja-Delta tace ‘yan arewa da kabilar yarabawa da suke Niger Delta su bar musu yankinsu kafin kamawar watan Oktoba.

Kungiyar ta bada sanarwa ta yanke shawara a taron da tayi a Akwa Ibom me suna ‘hadin gwiwar magabtan Niger Delta koma kai hare-hare a ranar 10 ga Satumba, ‘yan arewa da yarabawan da ke yankin su bar yankin kafin 1 ga Oktoba, 2017.'

Bayan tattaunawar da kungiyar tayi, ta yanke shawarar mallakar rijiyoyin mai a karkashin yankin Niger Delta daga Satumba.

Taron da PANDEF suka yi da Mukaddashin shugaban kasa an yi ne don a yaudari ‘yan Niger Delta. Muna so mu sanar da Mukaddashin shugaban kasa, wanda ya gana da su basu da ikon kawo karshen rikicin Niger Delt , don da haka baza su wakilci mutanen mu ko magana da yawun mu ba.

Wata kungiyar Neja Delta ta sake bada wa'adin abar musu yankinsu a watan Oktoba
Wata kungiyar Neja Delta ta sake bada wa'adin abar musu yankinsu a watan Oktoba

‘Kungiyar sun bukaci a basu damar kula da albarkatun da ke yankin a karkashinsu. Muna kira ga gwamnatin tarayya ta mika mana gabadaya rijiyar mai da take karkashin ‘yan arewa da yarabawa. Duk wani kampani da ke aiki da rijiyar mai su tattara kayansu zuwa Oktoba.

Kungiyar ta kara kira ga NNPC ta mayar da hedikwatarta zuwa yankin Neja Delta sannnan shugaban NNPC din ma dole ya zama dan asalin yankinsu.

Duk wani kampanin mai da gas zasu mai da tushensu zuwa Niger Delta, da maslaha tsakanin mutanen Niger Delta wanda zai hada da biyan su albashi dai-dai da mutanen waje.

KU DUBA: Shahararren mawaki Rarara ya shiga hannun kwastam

Muna neman ‘yancinmu da mallakar Neja Delta, duk wasu ‘yan arewa da yarabawa da ke sana’a a yankin su tattara zuwa Oktoba.

Muna kira ga duk wata kungiya da ke kai hari da ta cigaba da fashe-fashe da hare-hare a bututun mai. Zamu cigaba da aiki da mutane masu himma da kishin yankinsu don samar da ‘yanci da ikon mallakar albarkatun yankinmu ta kowace hanya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel