Rashin Imani: Wani Uba da matarsa sun ɗaure yarinya a cikin buhu don yin tsafin kuɗi da ita

Rashin Imani: Wani Uba da matarsa sun ɗaure yarinya a cikin buhu don yin tsafin kuɗi da ita

- Wata yarinya ta rayu bayan kwashe kwanaki biyu cif cif daure cikin buhu

- Iyayen wannan yarinya ne suka jefar da yarinyar a kan hanya da nufin tsafi

Wasu ma’aurata, Nasiru Adeyemo da matarsa Idayat Adeyemo sun shiga komar jami’an Yansanda bayan da aka kama sud da zargin kokarin salwantar da rayuwar yarsu mai shekaru 7, Abibat Anike Adeyemo.

Yansanda sun Ankara da halin daa wannan yarinya ta shiga ne bayan da jama’a suka gulmata musu bayyanar wani farin buhu akan hanya, wanda yake a daure, inda ba tare da wata wata ba, Yansanda suka dira wajen.

KU KARANTA: Hotunan yadda ýaýan majalisar dokoki suka dambace a majalisa

Kaakain rundunar Yansandan jihar ASP Abimbolaa Oyeyemi yace samun labarin ya sanya DPO dake rike da yankin ya jagoranci tawagar yansanda zuwa wajen, idna suka tarar da buhun, kwance shi keda wuya suka tarar da yarinyar a ciki a sume, tare da yatsar ta na hannun dama a guntule.

Rashin Imani: Wani Uba da matarsa sun ɗaure yarinya a cikin buhu don yin tsafin kuɗi da ita
Mahaifin yarinyar da yarinyar a cikin buhu

Daga nan ne yansanda suka garzaya da yarinyar asibiti, inda aka ceto rayuwarta, bayan ta kwashe kwanaki 2 daure a cikin buhun, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Rashin Imani: Wani Uba da matarsa sun ɗaure yarinya a cikin buhu don yin tsafin kuɗi da ita
Yarinyar da iyayenta

Baya da farfado ne sai yarinyar ta shaida ma yansanda cewa mahaifinta da kishiyar babarta ne suka guntule mata yatsan hannunta, sa’annan suka daure ta a cikin buhun, suka jefar tun ranar juma’a data gabata.

Jin wannan labara ya sanya yansanda baza komarsu wajen neman iyayen wannan yarinya ruwa a jallo, inda suka samu nasarar kama su a ranar Lahadi 13 ga watan Agusta. Kuma tuni an fara bincike akansu.

Rashin Imani: Wani Uba da matarsa sun ɗaure yarinya a cikin buhu don yin tsafin kuɗi da ita
Uba da matarsa

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Kalli yadda aka kashe wani mai satar mutane:

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel