Abinda ya sa na kashe budurwata - Ma'aikacin Air Force Bernard Kalu

Abinda ya sa na kashe budurwata - Ma'aikacin Air Force Bernard Kalu

- Dan rudunar sojojin Najeriya da za'a kashe, Bernard Kalu, ya bayyana dalilin da ya sa ya kashe budurwar shi ​​Oladipupo Sholape

- Kalu ya ce yayi zargin Sholape cewa tana soyayya tare da wani mutum

- Ya ce ya riga ya yi alkawarin gabatar da ita a gaban mahaifiyarsa kan aure ba da daɗewa ba kamin mutuwar ta

Bernard Kalu, wanda aka sallame shi kuma aka yanke masa hukuncin kisa saboda kashe budurwarsa, mai aikin jirgin sama Oladipupo Sholape, ya ba da bayanai game da dalilin da yasa ya aikata laifin.

Kalu a cikin sanarwa ya shaida wa kotu cewa bai san lokacin da ya kashe Sholape ba.

Kalu ya ce ya yi zargin budurwarsa tana soyayya da wani bayan ya kuma yi alkawarin aurenta.

Ya kara da cewa a daren kafin ya aikata laifin, mahaifiyarsa ta shawarce shi ya mayar da hankali akan jarrabawarsa maimakon tunanin aure.

Abinda ya sa na kashe budurwata - Ma'aikacin Air Force Bernard Kalu
Abinda ya sa na kashe budurwata - Ma'aikacin Air Force Bernard Kalu

Ya ce kama ya fara lura da cewa budurwar tana janye wa daga gare shi.

Sai ya nemi gafara kuma suka ci gaba da soyayya da kyau har sai lokacin ranar haihuwar Sholape a watan Fabrairu, lokacin da suka yi fada akan rashin bata kyauta na rannan haihuwa.

Amma an samu an daidaita al'amarin.

Amma ranar 11 ga watan Maris, ya ce ya tafi gidanta a Corporal da Below Quarters inda Sholape ta samu gidan zama lokacin da ta gabatar da shi ga wani mutum mai suna Samuel Echo.

KU KARANTA KUMA: Majalisa za ta kafa dokar hana kalamun batanci – Bukola Saraki

Kalu ya ce nan da nan yayi zargin Sholape tana da dangantaka da Echo.

Ya sami lokaci shi kadai don duba wayar tarho ta Sholape don ganin sakonnin da ke wayarta.

Ya ce da zarar Sholape ta shigo daga cikin ɗakin abinci inda ta ke yin abincin, sai ta yi fushi kuma ta tambayi dalilin da ya sa yake duba mata waya.

Amma da ya tambayeta game da abubuwan da ya gani a kan wayarta, Kalu ya ce Sholape ta amsa da cewa, "yanzu ka sani, to, sai me kuma."

Kalu ya ce ya yi fushi, nan da nan ya fara ciwon kai kuma ba shi da wani zaɓi sai ya koma gidansa barci.

Ya ce lokacin da bacci ya fita a idanunsa,shi ne ya kwasa kayansa ya sa a dakin abokinsa, shine sai kawai ya ga kansa a cikin ɗakin ajiya.

Ya ce ya karbi kansa bayan da aka gaya masa cewa ya kashe budurwarsa. Har ila yau, bai yarda ya kashe Sholape ba.

Duk da haka, shugaban kotu na rukuni, Elisha Bindul ya sami Kalu a cikin shida daga cikin laifuffuka takwas da aka yi masa.

Bindul ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Legit.ng a baya ya ruwaito cewa an yanke wa Kalu hukuncin kisa duk da rokon da akayi cewa shi ne mai ba da taimako ga iyalinsa.

Lauyan Kalu,Abimiku Ewuga ya ce zai daukaka karar zuwa babban kotun shari'ar na sojoji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel