Ta kama mijinta ya na fasikanci da 'yar su

Ta kama mijinta ya na fasikanci da 'yar su

Dubun wani mutum a jihar Katsina ta cika bayan da matar sa ta damke shi dumu-dumu ya na aikata fasikanci da 'yar su mai shekaru 14 a duniya

Wata mata, Mariya Inusa, mai shekaru 35 a duniya, wadda mazauniyar kauyen Rafin-Makadi ce, a karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina, ta shigar da karar mijin ta Inusa Aliyu wajen 'yan sanda, da laifin aikata fasikanci da 'yar su mai shekaru 14.

Mariya ta tabbatar da wannan ta'asa da mijin ta yake aikatawa bayan da ta kama shi dumu-dumu a cikin laifi, inda ta garzaya wajen 'yan sanda.

Ta bayyanawa 'yan sanda cewa, daman ta jima ta na zargin wannan abu, amma gashi yau ta gani da idonta da dubu ta cika kuma kuma daman ance gani ya kori ji domin ya tabbatar ma ta da zargin da ta jima ta na yi.

Ta kama mijinta ya na fasikanci da 'yar su
Ta kama mijinta ya na fasikanci da 'yar su

Mariya ta kara samun tabbaci daga wajen 'yar ta su bayan da ta titsiye ta akan sai ta fada mata a gaskiyar lamarain inda ita kuma ba ta boye ma ta komai ba.

KU KARANTA: Watanni 8 a gidan Kaso – Wani mutum ya saci buhu 90 na siminti

Kakakin 'yan sandan jihar Katsina, DSP Gambo Isah, ya tabbatar da cewa, Inusa yana nan a hannun su domin cigaba da bincike kafin su tura shi gaban alkali.

Inusa ya amsa laifin da ake tuhumar shi da shi, kuma ya ce wani dan duba ne ya ba shi wani lakani kuma idan bai aikata fasikanci da 'yar shi ba to kuwa lakanin zai karye.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel