Amfanin ayaba guda 7 a jikin mutum

Amfanin ayaba guda 7 a jikin mutum

Ayaba ta na daya daga cikin kayan itatuwa da aka fi amfani da su a duniyar nan saboda wasu kwararan dalilai. Cin ayaba yana rage hawan jini da kuma bayar da kariya ga cututtukan daji da na asma.

Akwai kimanin kasashe 107 da su ke noman ayaba kuma hakan ya sanya su cikin jerin kasashe da suke samun ribar kudi na amfanin gona. Kasar Amurka su na amfani da ayaba sama da yadda idana ka hade amfanin da su ke yi da lemo da tufa.

Yadda ake samun karuwar amfani da ayaba a duniya, tambayoyin da mutane su ke yi akan fa'idar ayaba ba ya bayar da wani mamaki.

Amfanin ayaba guda 7 a jikin mutum
Amfanin ayaba guda 7 a jikin mutum

Fa'idojin ayaba guda bakwai a jikin dan Adam

1. Hawan jini

Sanadiyar sunadarin potassium a cikin ayaba, ya sanya ta na matukar tallafawa wajen rage hawan jini ga wadanda su ka manyanta.

2. Asma

A wani bincike da aka gudanar a kwalejin ilimi ta kasar Landan, ya nuna cewa yara da suke cin ayaba kwara guda a rana, tana hana su kamuwa da cutar asma.

3. Cutar daji (Kansa)

Amfani da ayaba a shekaru biyun farko na rayuwar mutum yana hana kamuwa da cutar daji ta cikin jini. Akwai sunadarin vitamin C da yake yakar duk wasu kwayoyin cutar daji a jikin mutum.

4. Ciwon Zuciya da koda

Ayaba tana kunshe da sunadaran fiber, potassium, vitamin C da B6 wadanda suke bayar da kariya ga lafiyar zuciya. Binciken asibitin St Thomas dake garin Tennessee a kasar Amurka, ya bayyana cewa, wadannan sundaran su na taimakawa wajen yakar cututtukan zuciya da na koda a jikin a dan Adam.

KU KARANTA:Yadda miliyoyin mutane su ke fama da rashin abinci a Jamhuriyyar Kongo – UN

5. Ciwon sikari

Bincike ya nuna cewa cin ayaba yana rage yaduwar ciwon sikari a cikin jini sanadiyar sunadarin fiber da yake kunshe a cikin ayaba.

6. Ciwon ciki

Ba shakka ayaba tana magance cutar gudawa da take addabar mutane, domin duk wani mai gudawa idan ya ci ayaba to kuwa yana samun waraka ta hanyar sunadarin potassium da yake daure cikin mutum.

7. Kaifin basira

Wani sabon bincike ya bayyana cewa, akwai sunadarin amino acid mai suna tryptophan da yake bunkasa kaifin basira na kwakwalwar dan Adam.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel