Gidaje 1000 sun salwanta a jihar Bauchi sanadiyar ambaliyar ruwa

Gidaje 1000 sun salwanta a jihar Bauchi sanadiyar ambaliyar ruwa

Sanadiyar ambaliyar ruwa a jihar Bauchi, fiye da gidaje 1000 sun rushe wanda gwamnatin jihar ta ke iya ka cin bakin kokarinta wajen sanyaya zukatan wadanda abin ya shafa

Fiye da gidaje 1000 sun rushe sanadiyar ambaliyar ruwa a kauyukan, Faggo, Yana da sauransu, a karamar hukumar Shira dake jihar Bauchi.

Sakataren gwamnan jihar Bauchi, Abubakar Al-Sadique ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Alhamis din da ta gabata.

Ya ce, gwamnan jihar, Muhammad Abubakar, ya kai ziyara wannan yankunan da abin ya shafa kuma ya bayar da tallafin abinci da kayan masarufi na kimanin Naira miliyan 11 don agazawa wadanda su ka shiga mawuyacin hali.

Gidaje 1000 sun salwanta a jihar Bauchi sanadiyar ambaliyar ruwa
Gidaje 1000 sun salwanta a jihar Bauchi sanadiyar ambaliyar ruwa

A cewar Sakataren, gwamnan ya nuna damuwarsa kwarai akan faruwar wannan a jihar gaba daya, kuma gwamnatin ta tanadar da tallafin ne ko ya dan sanyaya zukatansu wadanda abin ya shafa.

KU KARANTA: Abinda ya sa na kashe budurwata - Ma'aikacin Air Force Bernard Kalu

Ya kara da cewa, dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Shira, Auwal Hassan, ya roki gwamnan da ya samar da gine-gine na hanyoyi da magudanan ruwa wanda zai kawo karshen faruwar wannan abu a gaba.

A yayin haka ne kuma, wani sakatare na dindin, ya umarci mazauna yankunan da abin ya shafa, da su kauracewa yankunan kafin gwamnati ta kallama gyara.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel