An haifi wani jariri da juna biyu a kasar Indiya

An haifi wani jariri da juna biyu a kasar Indiya

- A can kasar Indiya kuma an haifi wani jariri da juna biyu, inda binciken likitoci ya bayyana cewa mahaifiyar wannan jariri ce ta yi rashin sa'ar inda tagwayen 'ya'yan ta daya ya shige cikin daya

- Likitoci sun yiwa wannan jariri tiyaya kuma sun yi nasarar cire juna biyun dake cikin sa

Wani abun al'ajabi da ya faru a kasar Indiya, inda su kan su likitoci suka dinga mamakin yadda wannan abun ya faru domin kuwa an haifi wani jariri da juna biyu.

Likitoci masu amfani da na'ura wajen daukar hoton cikin jikin mutum sun bayyana cewa, sun gano wata halittar ta mutum a cikin cikin jaririn tun a farkon watan Yulin da ya gabata, wanda shi kan shi wannan jariri yana cikin mahaifiyar shi 'yar shekaru 19.

Binciken likitoci ya bayyana cewa, mahaifiyar wannan jariri ta samu juna biyu ne na tagwaye, inda aka yi rashin sa'a daya ya shige cikin daya wanda ya sanya jaririn ya daina girma tun makonni sha uku a cikin mahaifiyar ta sa.

An haifi wani jariri da juna biyu a kasar Indiya
An haifi wani jariri da juna biyu a kasar Indiya

Bayan haihuwar wannan jariri a ranar 20 ga watan Yuli, wani asibiti mai sunan Bilal Hospital a gundumar Thane dake babban birnin Mumbai na kasar Indiya, sun yiwa wannan jariri tiyata inda suke cire wannan juna biyu dake cikin shi.

KU KARANTA: Abuja: A karshe dai za a sassanta tsakanin gwamnan Kogi da Melaye

Wani kwararren likitan yara Thorat, wanda ya yiwa jaririn tiyata, ya bayyana cewa, juna biyun dake cikin jaririn namiji ne kuma tsayin shi ya kai inci bakwai da kuma nauyi na giram 150.

Babu wata damuwa ko matsala da ta ke tattare da mahaifiyar wannan jariri da da jaririn na ta kuma su na cikin koshin lafiya da kulawa a asibiti, a cewar wata likitan mata Nicahali da ta labartawa manema labarai.

Nichilani da Thorat sun bayyana cewa, kawowar wannan lokaci a duniya, an samu faruwar ire-iren haka sau 100 ne kacal, kuma hasashe ya nuna cewa za a iya samun iren wannan abu a duk bayan haihuwa 500, 000 da ta zo da rai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://www.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel