Don Allah ka rabu da Ibo da Yarbawa su kafa kasar su - Matasan Arewa sun roki Buhari

Don Allah ka rabu da Ibo da Yarbawa su kafa kasar su - Matasan Arewa sun roki Buhari

Hadaddiyar kungiyar gamayyar matasan Arewa ta nuna rashin jin dadin ta ga kalaman da shugaba Buhari yayi a cikin jawabin da yayi wa yan Najeriya game da tabbatar da kasar nan ta zauna a dunkule.

Kungiyar a cikin wata sanarwa da ta fitar ta roki gwamnatin ta Buhari da ta duba girman Allah ta gudanar da zaben raba gardama a yankin kamar yadda suka bukata domin sanin ainihin sahihancin mukatar ta su ta ballewa daga Najeriyar.

Don Allah ka rabu da Ibo da Yarbawa su kafa kasar su - Matasan Arewa sun roki Buhari

Don Allah ka rabu da Ibo da Yarbawa su kafa kasar su - Matasan Arewa sun roki Buhari

NAIJ.com ta samu cewa shugaban hadakar gamayyar kungiyoyin na matasan arewa ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta bullo da sahihiyar hanyar da za'a bi wajen raba kasar a maimakon dagewa kan dole sai an zauna tare ko da kuma babu anfanin yin hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a jiya ma dai shugaban ya wajabtawa shugabannin rundunonin tsaron Najeriya da su tabbatar da maido da doka da oda a kasar tare kuma da hukunta duk wani hatsabibin da ya nemi ya tayar da kayar ba.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
NAIJ.com
Mailfire view pixel