Shugaban Sojin sama ya gargadi masu yada kiyayya ta shafukan sada zumunta

Shugaban Sojin sama ya gargadi masu yada kiyayya ta shafukan sada zumunta

- Babban kwamandan sojin sama, Sadiq Abubakar ya gargadi masu yada kiyayya ta shafukan sada zumunta

- Yayi kira ga manyan kasa da su gargadi matasa don daina anfani da hanyar sada zumunta ta hanyar da bai dace ba

- Shugaba Buhari yayi jawabi a dawowarsa kasa kan cigaba da hadin kan Najeriya

Babban kwamandan sojin sama na kasa, Sadiq Abubakar, ya gargadi 'yan Najeriya a kan su guji yin amfani da kafafen sada zumunta na zamani masu matsuguni a yanar gizo domin yada labaran karya da kalamai da ka iya raba kan jama'ar kasa.

Mista Abubakar ya bayyana hakan ne ranar talata a Abuja yayin wata bita mai taken 'sarrafawa da yada labarai' da a ka gudanar domin sojin sama.

Shugaban Sojin sama ya gargadi masu yada kiyayya ta shafukan sada zumunta

Shugaban Sojin sama ya gargadi masu yada kiyayya ta shafukan sada zumunta

'Duk muna sane da yadda wasu bata gari ke amfani da kafar sada zumunta na zamani domin yada kalamai masu guba, rura wutar rikici, yada jita-jita, da karya.' a fadin Kwamandan.

'Yin hakan ba abinda zai haifawa kasar nan da mai ido ba ne, don haka ina kira ga duk masu ruwa da tsaki da suke son cigaban kasar nan da su dukufa domin ganin an daina amfani da kafafen zumuntar ta hanyar da bai dace ba'

DUBA WANNAN: Kotu ta haramta saki uku na farat-daya

A jawabin da Shugaba Buhari yayi na dawowarsa, ya bayyana cewar 'gwamnatinsa ba zata lamunci duk wani yunkuri na raba kan kasa ba.'

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
NAIJ.com
Mailfire view pixel