Manoma 22,000 ne zasu ci moriyar tallaffin babban bankin CBN da kuma Bankin Sterlin a jihar Kebbi

Manoma 22,000 ne zasu ci moriyar tallaffin babban bankin CBN da kuma Bankin Sterlin a jihar Kebbi

Tun bayan hawansu mulki a shekarar 2015, shugaba Buhari ya sha alwashin kora kowa gona, da sanya wa Najeriya zimmar dogaro da kai ta fannin abinci na gida, domin samar da ayyukan yi, ga samari, da isasshen abinci ga kasa, da tallafi ga manoma.

Babban bankin Najeriya CBN da Sterlin Bank na hadin gwiwa don tallafawa manoma kusan dubu 22, saboda habaka noma da samar da abinci ga kasa.

Manoma 22,000 ne zasu ci moriyar tallaffin babban bankin CBN da kuma Bankin Sterlin a jihar Kebbi
Manoma 22,000 ne zasu ci moriyar tallaffin babban bankin CBN da kuma Bankin Sterlin a jihar Kebbi

'Hoto daga jaridar Inside Arewa'

Akalla manoma 22,000 ne a jihar zasu amfana daga tallafin da baban Bankin Najeriyar zai bada domin bunkasa noman shinkafa a kasar, shi tallafin ya samu asali ne daga wata hukumar taimaka wa manoma mai suna NIRSAL. Kuma bankin Sterlin ne zai raba wannan tallafin ga manoman.

A tataunawa da Jami’an na NIRSAL a jihar Kebbi, shugaban kasuwanci na bankin mai suna Adewale Adebowale yace zasu tallafa wa manomane da bashi naira 250,000. Bashin kuma zai tallafa wa manoman wajen samun kayan aiki cikin saukin zuwa ga wajajen nomansu.

Adebowale yaci gaba da cewa shi bankin nasu tare da mutanen da suka hada hannun gwiwan tafiyar da aikin cikin sauki, shirye suke wajen tabatar da sun samu abubuwan da yakamata wajen manoman, domin tabarta da su manoman su samu amshi kudin daga jami’an bankin cikin sauki. ⁠⁠⁠⁠

DUBA WANNAN: An kasa samun matsaya kan batun ASUU, amma gwamnati na shirin fadin matsayarta

A yanzu bankin ya tantance manoma 15,000, abin da ya rage shine shigar da lambobinsu na BVN domin samun damar basu katin cirar kudin ta aljihun ATM.

Ya kara da cewa bankin ya ware wasu jami’ai domin tabbatar da cewa manoman da ke kauyuka sun samu damar cirar kudaden su batare da amafani da wata tangarda ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel