Zaben Anambra: Nasarar jami'iyyar APC zai sa kabilar ibo su rungumi APC - Buhari Support Organization

Zaben Anambra: Nasarar jami'iyyar APC zai sa kabilar ibo su rungumi APC - Buhari Support Organization

- Kungiyar masu goyon bayan Buhari suna so a zabi gwamnan Anambra daga jam'iyyar APC

- Samun nasarar Nwoye zai zame wa 'yan jihar alheri a gare su

- Amma wasu basa goyon bayan zabe daga jam'iyyar APC

Kungiyar masu goyon bayan Shugaba Buhari ta kudu maso gabashin Najeriya, ta bawa 'yan jihar Anambra sanarwar cewa kar su sake su zabi wata jam'iyya face jam'iyyar APC a zaben gwamnoni mai zuwa.

Kungiyar ta bada shaidar lallai babban kuskure ne a zabi wani shugaba banda Tony Nwoye na jam'iyyar APC. Wanda kungiyar ta misalta shi a matsayin mutum mai kaifin basira, mai son jama'a wanda yake da alamun cin zaben gwamnonin da za a yi watan Nuwamba.

Zaben Anambra: Nasarar jami'iyyar APC zai sa kabilar ibo su rungumi APC - Buhari Support Organization

Nasarar jami'iyyar APC zai sa kabilar ibo su rungumi APC

Kungiyar ta yi kira ga masu goyon bayan dan takarar Honorabul Nwoye da su hadu don tsayawa tsayin daka don ganin Nwoye ya ci zabe, domin kuwa samun nasarar Nwoye samun nasara ne ga dukkan kabilar su.

DUBA WANNAN: El-Rufai ba shi da ladabi, bai san girman manya ba-Edwin Clarke

Samun nasarar Nwoye zai samar da abubuwa da yawa kamar Kwamishinoni, Mambobi na jam'iyyu da ayyuka da dama ga wanda suka bada goyon baya har da sauran mutanen wasu jam'iyyar.

A yayin da wasu wanda suka dade a jam'iyyar APC ta jihar Anambra suke nuna rashin jin dadin su domin ware su da aka yi, suna ganin musamman tsohuwar kungiyar CPC.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kana kana da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36
NAIJ.com
Mailfire view pixel