Yadda Allah ya cika burin matata wacce ta mutu a Makkah bayan aikin hajjin 2017 – Dan Najeriya

Yadda Allah ya cika burin matata wacce ta mutu a Makkah bayan aikin hajjin 2017 – Dan Najeriya

Wani dan Najeriya da matarsa ta mutu bdullahi Mahuta ya bada labarin yadda Allah ya amsa addu’ar matarsa.

A cewarsa, burin matarsa na karshe shine Allah ya karbi ranta a Makkah. Mahuta yayi bayanin cewa matarsa ta rasu bayan ta kammala aikin hajji a wannan shekarar.

A wani rubutu da Mahuta ya wallafa a shafin Facebook ya bayyana cewa matarsa ta fada ma mahaifiyarta burinta na karshe kafin ta tafi aikin hajji.

Ya rubuta: “Furucin ta na karshe ga mahaifiyarta a lokacin da zata tafi aikin hajjin bana shine: Mama, fata na idan na gama aikin Hajji na lafiya, ace Allah ya dauki rai na a can.”

KU KARANTA KUMA: 2019: Babu wanda ya san zuciyar Buhari a yanzu – Shehu Sani

Yadda Allah ya cika burin matata wacce ta mutu a Makka bayan hajjin 2017 – Dan Najeriya
Yadda Allah ya cika burin matata wacce ta mutu a Makka bayan hajjin 2017 – Dan Najeriya

Ya kara da cewa Allah ya amsa addu’arta sannan ya cika mata burinta na mutuwa a kasa mai tsarki wato Makkah, ya kara da cewa Allah ya yafe mata dukkan kurakuranta.

KU KARANTA KUMA: Bana tunanin Buhari na da butulci – Inji Aisha Alhassan bayan ziyarar ta Aso Rock

Mahuta ya rubuta: “Sannan Allah ya amsa addu’arta ya kuma cika mata burin ta. Za a yi jana'izar ta a Haram probably gobe in shaa Allah. Allah ya raya mana Samha.”

Allah mai iko!

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel