Sunayen mutane 20 da suka fi kowa kyauta da sadakar dukiyarsu a duniya

Sunayen mutane 20 da suka fi kowa kyauta da sadakar dukiyarsu a duniya

Legit.ng ta kawo muku jerin sunayen masu kudin da suke sadaka da kuma kyautar da dukiyar da Allah ya azurta su da ita.

Wani hamshakin mai kudi na kasar Amurka Andrew Carnegie ya ce, "babu mutumin da zai yi arziki face sai ya kasance sanadiyar azurta wasu".

Da yawa daga cikin ma su kudin da suke raba dukiyar ta su sun tafi akan yardar cewa, su na yin hakan ne domin kyautatawa da kuma yin sadaka ga mabukata, kuma hakan zai taimaka wajen kawo wani dan sauyi komai kankantarsa ga rayuwar wadanda suka baiwa dukiyar ta su.

Sunayen mutane 20 da suka fi kowa kyauta da sadakar kudi a duniya
Sunayen mutane 20 da suka fi kowa kyauta da sadakar kudi a duniya

Ga jerin Sunayen attajirai 20 da suke ciyar da wasu daga cikin dukiyar da Allah ya basu, tare da adadin kudin da suka kyautar da kuma kasashen su.

20. Dietmar Hopp - Dalar Amurka biliyan 1 (Kasar Jamus)

19. Pierre Omidgar - Dalar Amurka biliyan 1 (Kasar Amurka)

18. Michael Dell - Dalar Amurka biliyan 1.1 (Kasar Amurka)

17. James Simons - Dalar Amurka biliyan 1.2 (Kasar Amurka)

16. Ted Turner - Dalar Amurka biliyan 1.2 (Kasar Amurka)

15. Jon Huntsman Sr. - Dalar Amurka biliyan 1.2 (Kasar Amurka)

14. Li Ka-Shing - Dalar Amurka biliyan 1.2 (Kasar Sin)

13. Mark Zuckerberg - Dalar Amurka biliyan 1.6 (Kasar Amurka)

12. Paul Allen - Dalar Amurka biliyan 2 (Kasar Amurka)

11. Michael Bloomberg - Dalar Amurka biliyan 3 (Kasar Amurka)

10. George Kaiser - Dalar Amurka biliyan 3.3 (Kasar Amurka)

KU KARANTA KUMA: Dalilai 3 da za su sanya kara riko da shayi na koren ganye

9. Eli Broad - Dalar Amurka biliyan 3.3 (Kasar Amurka)

8. Carlos Slim Helu - Dalar Amurka biliyan 4 (Kasar Mexico)

7. Gordon Moore - Dalar Amurka biliyan 5 (Kasar Amurka)

6. Suleiman Bin Abdul Aziz Rajhi - Dalar Amurka biliyan 5.7 (Kasar Saudiya)

5. Charles Francis Feeney - Dalar Amurka biliyan 6.3 (Kasar Ireland)

4. Azim Premji - Dalar Amurka biliyan 8 (Kasar India)

3. George Soros - Dalar Amurka biliyan 8 (Kasar Hungary)

2. Warren Buffet - Dalar Amurka biliyan 21.5 (Kasar Amurka)

1. Bill Gates - Dalar Amurka biliyan 27 (Kasar Amurka)

Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel