Jami’an kwastam sun kama muggan makaman bindiga sama da 1000

Jami’an kwastam sun kama muggan makaman bindiga sama da 1000

- Hukumar kwastam ta kama bindigogi a tashar jirgin ruwa

- Makaman na da karfin kashe jama'a da dama a lokaci daya

A ranar 6 ga watan Satumba ne hukumar yaki da fasa kauri ta kasa, NCS, ta kama wani katon sunduki mai dauke da makaman bindigu guda 1,100, kamar yadda shugaban hukumar ya bayyana a ranar 11 ga watan Satumba.

Wannan kamen ya kawo yawan bindigun da hukumar ta kama a shekarar nan zuwa 2110, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito shugaban hukumar Hamid Ali na shaidawa manema labaru.

KU KARANTA: Rikicin Duniya da mai rai ake yi; Ibtila’i ya faɗa kan wani Ango da Amaryarsa a ranar bikinsu

Jami’an kwastam sun kama muggan makaman bindiga sama da 1000
Bindigun

Hamid Ali yace an shigo da bindigun ne daga kasar Turkiyya, sa’annan kowace bindiga na iya kashe mutane da dama a tashi guda, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Jami’an kwastam sun kama muggan makaman bindiga sama da 1000
bindigun

Shugaban kwatsam reshen Tin Can Island, Bashar Yusuf yace da fari wasu baragurbin jami’an kwatsam sun bude ma sundukin hanyar wucewa, amma daga bisani ya matsa lallai sai an binciki sundukin gaba dayansa.

Jami’an kwastam sun kama muggan makaman bindiga sama da 1000
Sundukin

Zuwa yanzu an cafke mutane 2 dake da hannu cikin wadanda keda hannu a shigo da makaman, sa’annan shugaban hukumar yace ya dace a fadada bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel