Mutum 30 sun rasa ran su a mummunan hatsarin mota a hanyar Legas-Ibadan

Mutum 30 sun rasa ran su a mummunan hatsarin mota a hanyar Legas-Ibadan

- Ana kyautata zaton gudun hauka ne ya janyo hatsarin

- Karin mutum 10 sun jikkata

- Ana kira ga direbobi da su rage gudu, da kuma tafiyar dare.

Mai magana da yawun bakin ma'aikatar lafiyar hanya (FRSC), Bisi Kazeem, ya baiyanawa manema labarai cewa an sami mummunan hatsarin motar a ranar Alhamis da daddare a kan titin Legas zuwa Ibadan, wanda ya yi sanadiyyar rayuka 30, da kuma jikkatar karin mutane 10.

Mummunan hatsari da ya faru a kan babbar hanyar Legas-Ibadan ya yi sanadiyyar rayukan mutane 30
Hatsarin mota a kan babbar hanya

Ya ce hatsarin ya faru wajen karfe 8 na dare a wajen mahakar Elebolo dake kan hanyar zuwa Ibadan.

"Hatsarin ya auku ne tsakanin bas biyu, duk kirar Mazda, a yayin da suka rufta wa juna. Muna kyautata zaton gudun hauka ne ya janyo hakan.

"Ina kira ga direbobin mota da su dau nasihar shugaban mu, Corp Marshal Dr. Boboye Oyeyemi, da yake cewa a rage yin tafiyar dare, da kuma yin mumunan gudu."

DUBA WANNAN: 'Yan matan Chibok da aka ceto zasu shiga babbar jami'a a Najeriya

Mista Kazeem ya ce ma'aikatan FRSC sun kai dauki na cikin gaggawa wajen, inda aka garzaya da wadanda suka jikkata asibitocin UCH da Adeyoyo Yemetu duk a Ibadan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, a tuntube mu a:

labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel