Amurka ta ki taimakawa Musulman Myanmar da ke Bangladesh

Amurka ta ki taimakawa Musulman Myanmar da ke Bangladesh

- Shugaba Donald Trump ya ki taimakawa tsirarun Musulman Burma

- Shugaban yayi mursisi game da bayin Allah da ke cikin mawuyacin hali

- Musulmai da dama daga Myanmar sun tsere zuwa Kasar Bangladesh

A halin yanzu tsirarun Musulmai da dama da ke Kasar Rohingya sun tsere zuwa Kasar Bangladesh domin gudun hijira.

Amurka ta ki taimakawa Musulman Myanmar da su kayi gudun hijira
Sheikh Hasina Wazed ta kasar Bangladesh

Shugaban kasar Amurka yayi mursisi game da mutanen na Rohingya da kisan gillar Sojoji ta sa su ka bar Kasar yayin da su ka gana da Firayim Ministar Bangladesh Sheikh Hasina Wazed. Trump ya nemi jin halin da mutanen ke ciki amma kuma bai yi wani yunkurin agaza masu ba.

KU KARANTA: Erdogan zai taimakawa Musulman Burma da ke gudun hijira

Ita dai Shugabar Bangladesh tace ba za ta roki Shugaba Trump din ba domin bai da niyyar taimakawa mutanen da su ka fake a Kasar ta. Sheikh Wazed tace ko da kasar ta ba ta da arziki za ta cigaba da taimakawa 'yan uwan su da su ka tsere zuwa Kasar ta.

Dazu kun ji cewa a iya cewa kwalliya ta fara biyan kudin sabulu bayan jawabin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a taron Majalisar Dinkin Duniya game da mutanen na Myanmar wanda yanzu Kasar Birtaniya za ta daina horar da Sojojin Kasar Burma.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Za ka iya zama da sirikan ka a gida guda?

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel