Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kaduna ya zama Gwamna

Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kaduna ya zama Gwamna

- Honarabul Dr. Aminu Shagali ya zama Gwamnan Jihar Kaduna

- A halin yanzu Gwamnan Jihar da Mataimakin sa sun yi tafiya

- Gwamnan yana Ingila yayin da Mataimakin sa ya wuce Amurka

Kakakin Majalisar Jihar Kaduna Rt. Hon. Dr. Aminu Abdullahi Shagali ya zama Gwamnan Jihar Kaduna na rikon kwarya a Jihar.

Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kaduna ya zama Gwamna
Dr. Shagali ya zama Gwamnan rikon kwarya

Honarabul Aminu Shagali wanda shi ne mai rike da matsayi na uku a Jihar bayan Gwamna da Mataimakin sa. Yanzu haka Gwamnan Jihar Malam Nasir El-Rufai yana kasar Birtaniya a inda yayi wani jawabi game da yi wa Najeriya garambawul a dakin taro na Chatham House.

KU KARANTA: Gwamna Dankwambo ya karyata cewa ya daure wasu ma'aikata

Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kaduna ya zama Gwamna
Gwamnan Jihar Kaduna a gidan tarihi na Chatham House

Haka kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Arch. Bala Bentex yana kasar Amurka inda yake wakiltar Jihar a wani taro na musamman na Majalisar Dinkin Duniya watau UN. Yanzu haka dai Kakakin Majalisa ne ke rike da Jihar na rikon kwarya kafin Gwamnan su dawo.

Dama tun jiya ku ka ji labarin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tattara ya tafi Landan bayan taron Majalisar Dinkin Duniya domin ganin Likitocin sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Mazauna Jihar Abiya sun yi magana game da Rundunar Soji

Asali: Legit.ng

Online view pixel