Farawa da iyawa! Jaruma Rahma Sadau ta lashe kyauta a masana'antar fina-finan kudu

Farawa da iyawa! Jaruma Rahma Sadau ta lashe kyauta a masana'antar fina-finan kudu

Farawa da iyawa fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood da a kwanan baya aka dakatar da ita da kuma ta shilla zuwa masana'antar fina-finan kudancin kasar nan na Nollywood tuni har ta fara lashe kyauta.

Mun samu dai cewa jarumar yanzu haka an lissafa ta a matsayin jarumar da ta lashe kyautar nan ta BON a rukunin yan wasa sabbin jini tare da wani jarumin kuma Namiji mai suna Gbenro.

Farawa da iyawa! Jaruma Rahma Sadau ta lashe kyauta a masana'antar fina-finan kudu
Farawa da iyawa! Jaruma Rahma Sadau ta lashe kyauta a masana'antar fina-finan kudu

KU KARANTA: FIFA ta fara bincikar Chelsea da Man utd

Legit.ng dai ta samu cewa jarumar ta sanar wa da duniya wannan nasarar da ta samu ne a shafin ta na Instagram inda ta bayyana cewa tana yiwa dukkan magoya baya da kuma masoyanta jinjinar ban girma.

A wani labarin kuma fitacciyar jarumar nan ta wasan Hausa a masana'antar Kannywood mai suna Hadiza Gabon ta fara fitowa a cikin fina-finan turanci na kudancin kasar nan watau Nollywood.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel