A Kasar Turkiyya, za'a fara koyar da yara ilimin Jihadi

A Kasar Turkiyya, za'a fara koyar da yara ilimin Jihadi

- Gwamnatin kasar Turkiyya mai kishin Islama zata maye gurbin koyar da ilimin kimiyya na evolution, dana jihadi

- Yunkurin hakan ya jawo suka da zanga-zanga musamman daga jam'iyyun hamayya na AKP da CHP

- Kawunan kungiyoyin malamai ma sun rabu kan muhawarar dacewar koyar da ilimin jihadin ko sabanin hakan

Gwamnatin kasar Turkiyya mai kishin Islama zata maye gurbin koyar da ilimin kimiyya dana jihadi a wani yunkuri daya jawo suka da zanga-zanga musamman daga jam'iyyun hamayya na AKP da CHP da suka zargi gwamnatin shugaba Tayyip Erdogan da kokarin gurbata tunanin yara ta hanyar canja manhajar ilimin kasar dana masu tsatssauran ra'ayin islama irin wanda ya jefa gabas ta tsakiya cikin rikici.

A Kasar Turkiyya, za'a fara koyarda yara ilimin Jihadi
A Kasar Turkiyya, za'a fara koyarda yara ilimin Jihadi

Ministan ilimin kasar ya ce "ya kamata a shigo da darasin jihadi ne a matsayin bangare na manhajar ilimi domin wani bangare ne na addinmu kuma nauyi ne da ya rataya a wuyanmu mu koyar da ko wanne abu ta yadda ya kamata tare da gyara abubuwan da aka yi wa mummunar fahimta".

Ministan ya ce za a karntar da ilimin kimiyya hadi dana batun halittar dan adam(evolution) a matakin sakandare, amma zasu canja masa suna. Saidai wani jami'in cibiyar garambawul din ilimi a kasar ta Turkiyya mai suna, Aysel Madra, ya ce yin hakan zai rudar da yara ne kawai.

DUBA WANNAN: An dakatar da malamin Islama a Saudiyya, bayan yayi katobara

Batun shigar da shigar da ilimin jihadi cikin manhajar ilimin naci gaba da jawo ce-ce-ku-ce a kasar Turkiyya. Kawunan kungiyoyin malamai ma sun rabu kan muhawarar dacewar koyar da ilimin jihadin ko sabanin hakan.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel