Duk mai rai mamaci ne: Allah yayi wa babban limamin jihar Legas rasuwa

Duk mai rai mamaci ne: Allah yayi wa babban limamin jihar Legas rasuwa

- Innalillah Wa'inna Ilaihi Raji'un

- Babban Lilamin Jihar Lagas Ya Rasu

- Allah ya gafarta masa, Allah ya baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Wani labarin jimami da ya same mu ba da dadewa ya nuna cewa Allah ya karbi ran babban limamin jihar Legas mai suna Haruna Akinola. Babban limamin dai ya rasu ne a jiya lahadi a can garin na Legas.

Duk mai rai mamaci ne: Allah yayi wa babban limamin jihar Legas rasuwa
Duk mai rai mamaci ne: Allah yayi wa babban limamin jihar Legas rasuwa

KU KARANTA: Yadda Saraki ya hana yan IPOB kunyatar da Buhari

Labarin da muka samu har ila yau da na nuni cewa ya rasu ne bayan ya sha fama da yar gajeruwar rashin lafiya inda yayi jinya a asibitin koyarwa ta jami'ar jihar Legas.

Legit.ng ta samu cewa tuni dai akayi jana'izar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar a jihar ta Legas kuma jana'izar ta samu halartar dubban mutane daga sassa daban-daban na jihar da ma kasar baki daya.

Haka ma dai tuni har an fara tururwa zuwa gidan mamacin domin yi ma iyalan sa ta'aziyyar sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel