Tufka da warwara: Ban taɓa alƙawarin gyara wutan Najeriya a wata 6 ba – Inji Fashola

Tufka da warwara: Ban taɓa alƙawarin gyara wutan Najeriya a wata 6 ba – Inji Fashola

- Ministan wuta da ayyuka ya musanta batun da ake yin a cewa wai yayi alkawarin gyara wuta cikin wata 6

- Ministan yace yana nufin wutan unguwar Lekki ne ban a Najeriya gaba daya ba

Ministan wuta da manyan ayyuka, BabaTunde Fashola ya musanta batun da ake yin a cewa wai yayi alkawarin gyara wuta cikin wata 6, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Ministan ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise, inda yace an kara gishin cikin maganar da yayi gishiri ne don ya dace da son ran wasu.

KU KARANTA: Cutar shan inna: Sarki Muhammadu Sunusi ya sha allurar shan inna (Hotuna)

“Na tuna inda na yi wannan batu, a lokacin ina amsa tambayar da wani mutumi ne yayi min akan yaushe zasu fara samun wuta? Yayin da muka kaddamar da wani katafaren inji da zai dinga baiwa unguwar Lekki wuta.

Tufka da warwara: Ban taɓa alƙawarin gyara wutan Najeriya a wata 6 ba – Inji Fashola
Fashola

“Amsar dana bashi itace zamu shiga hurumin kamfanuwa watsa wuta idan na bashi lokaci, amma idan hukumar lantarki ta kasa ta bamu izini, cikin watanni shidda zamu hada musu wuta.” Inji Fashola

A wani labarin kuma, wutan da Najeriya ke samarwa ya kai mega watt 70001 kamar yadda ministan samar da wutan lantarki, Babatunde Fashola ya bayyana.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel