Yan Boko Haram sun ƙaddamar da hari a Bama, suna halaka jami’in Ɗansanda

Yan Boko Haram sun ƙaddamar da hari a Bama, suna halaka jami’in Ɗansanda

- Wasu mayakan Boko Haram sun dira kauyen jihar Borno a ranar Juma'a

- Yan ta'addan sun kashe wani Dansanda da kuma yar gudun hijira

Wasu mayakan Boko Haram sun kaddamar da hari a kauyen Bama dake karamar hukumar Bama na jihar Borno, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito, a yayin kai harin, yan bindigan sun kashe wani dansanda, sa’annan wani harsashi daya kauce ya shafi wata yarinya yar gudun hijira, inda nan take ta fadi.

KU KARANTA: Atafau sai an aura min wanda nake so: Yarinyar Ganduje ta lashi takobin auren Bayarabe

Yan Boko Haram sun ƙaddamar da hari a Bama, suna halaka jami’in Ɗansanda
Yan Boko Haram

Kaakakin rundunar Soji ta 7, Laftanar kanal Kingsley Samuel ya bayyana haka cikin wata sanarwa, inda yace an kai harin ne a ranar Juma’a 29 ga watan Satumba, yayin da mayakan suka dira kauyen Bocobs, dake gab da garin Banki na karamar hukumar Bama.

Sai dai jin haka sai Sojojin Najeriya suka yi musu kwantan bauna, inda suka ragargaje su, suka kashe guda daga cikinsu, sa’annan da dama suka jikkata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel