Tsohon Kyaftin din Super Eagles ya bar tarihi a Ingila

Tsohon Kyaftin din Super Eagles ya bar tarihi a Ingila

- Dan wasan Najeriya Okocha ya kafa tarihi a tsohon Kulob din sa

- Kungiyar Bolton ta zabi Jay-Jay Okocha a matsayin gwarzon ta

- Shekaru 20 da su ka wuce zuwa yau ba a taba yin irin sa ba

An zabi tsohon Dan wasan Najeriya a matsayin babban Dan kwallon da ya taba taka leda a Kungiyar Balton ta Ingila.

Tsohon Kyaftin din Super Eagles ya bar tarihi a Ingila
Tsohon Dan wasan Super Eagles Okocha

Magoya bayan Kungiyar kwallon kafa ta Balton ne su ka zabi Tsohon Kyaftin din Najeriya kuma tsohon Dan wasan su Austin Jay Jay Okocha a matsayin babban Dan kwallon da ya taba bugawa Kungiyar wasa tun daga lokacin da aka gina sabon filin wasa na Reebok a shekarar 1997.

KU KARANTA: Tsohon Kocin Bolton ya jinjinawa Okocha

Shekaru 20 kenan da su ka wuce aka gina filin wasan na Reebok wanda har yau ba a samu wanda ya yi irin abin da tsohon Kyaftin din Super Eagles yayi ba. Daga cikin wadanda Jay Jay Okocha ya buge akwai irin su Ivan Campo da Youri Djorkaeff.

Okocha ya bar tarihi a wasu muhimman wasanni da ya bugawa Bolton a wasan karshen na cin kofin Carling da kuma Gasar Kofin UEFA na Turai lokacin yana ganiyar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel