Shekaru 57 da samun 'yancin kai: Jerin shugabannin kasa da Najeriya ta yi

Shekaru 57 da samun 'yancin kai: Jerin shugabannin kasa da Najeriya ta yi

A ranar Lahadi 1 ga watan Oktoban da ta gabata, kasar Najeriya ta cika shekaru 57 da samun 'yan cin kai daga mulkin mallaka na Turawan kasar Birtaniya. Shekaru uku bayan wannan samun 'yancin kai da kasa Najeriya ta yi, ta kuma zama jamhuriyya mai zaman kanta a shekarar 1963. A wannan shekara ne aka sauya tsarin shugabncin kasar, yayin da aka musanya gwamnoni masu shugabancin yankunan daban-daban wanda sarauniyar Ingila ta dora akan wannan mukami.

A ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960, kasar Najeriya ta samun 'yancin kai inda aka musanya wannan gwamnoni da shugaban kasa guda daya wanda zai mulki gaba daya jamhuriyyar ta na Najeriya.

Legit.ng ta bankado tarihi, inda ta kawo muku jerin shugabannin kasa da Najeriya ta yi tun daga ranar samun wannan 'yanci, ta kuma kawo sunayensu tare da ranar haihuwar da kuma tsawon lokuta da kowanensu ya diba akan kujerar mulki.

1. Dr Nnamdi Azikiwe (October 1, 1960 – October 1, 1963)

Dr Nnamdi Azikiwe (October 1, 1960 – October 1, 1963)
Dr Nnamdi Azikiwe (October 1, 1960 – October 1, 1963)

An haifi Dokta Nnamdi Azikiwe a ranar 19 ga watan Nuwamba na shekarar 1904, kuma shine shugaban kasa na farko da Najeriya ta yi. Azikiwe mutumin kabilar Ibo ne kuma mahaifarsa ta na garin Zungeru wanda a yanzu ya fada jihar Neja kenan.

Azikiwe ya jagoranci shugabancin kasar nan tun daga ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960 zuwa 1 ga watan Oktoba na shekarar 1963, wato shekaru uku kenan., ya kuma bar duniya a ranar 11 ga watan Mayu na shekarar 1996.

2. Gen Aguiyi Ironsi (January 16, 1966 – July 29, 1966)

Gen Aguiyi Ironsi (January 16, 1966 – July 29, 1966)
Gen Aguiyi Ironsi (January 16, 1966 – July 29, 1966)

An haifi Johnson Thomas Aguiyi Ironsi a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1924 a garin Umuahi dake jihar Abia. Ya shugabancin kasar nan a tsari irin na mulkin soja bayan juyin mulki da suka yi a ranar 15 ga watan Janairu na shekarar 1966, inda ya jagoranci kasar nan har zuwa 29 ga watan Yuli na shekarar 1966, wato dai watannin shi shida akan kujerar mulki.

An kashe manjo janar Ironsi a garin Ibadan dake jihar Oyo a ranar 29 ga watan Yuli na shekarar 1966 tare da Laftanal kanal Adekunle Fajuyi.

3. Gen Yakubu Gowon (August 1, 1966 – July 29, 1975)

Gen Yakubu Gowon (August 1, 1966 – July 29, 1975)
Gen Yakubu Gowon (August 1, 1966 – July 29, 1975)

Mahaifar Janar Yakubu Gowon ta kasance akauyen Lur na karamar hukumar Kanke dake jihar Filato, an kuma haifi shi a ranar 19 ga watan Oktoba na shekarar 1934.

Har yanzu tarihi ya nuna cewa babu wani shugaban kasa da shugabanci kasar nan a mafi karancin shekaru kamar na Gowon, domin kuwa ya karbi ragamar mulkin kasar nan tun yana dan shekaru 31 a duniya.

Ban da karancin shekaru, ba a taba samun shugaban kasar da ya yi jimawarsa akan mulki ba, domin kuwa ya mulki tun daga ranar 1 ga watan Agusta na shekarar 1966 har zuwa 29 ga watan Yuli na shekarar 1975, wato shekarunsa tara akan kujerar mulki.

Sai dai Gowon ya yi rashin sa'a wata kungiyar soji wanda Kanal Joe Nanven Garba ya jagoranta sun masa juyin mulki a yayin da ya tafi kasar Uganda domin halartar taron hadin kan kasashen Afirka a birnin Kampala.

4. Gen Murtala Muhammed (July 29, 1975 – February 13, 1976)

Gen Murtala Muhammed (July 29, 1975 – February 13, 1976)
Gen Murtala Muhammed (July 29, 1975 – February 13, 1976)

An haifi janar Murtala Ramat Muhammed a jihar Kano a ranar3 ga watan Nuwamba na shekarar 1938. Ya kuma shugabanci kasar nan cikin abinda bai wuci watanni 7 ba kafin ya fuskanci karshensa a ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976, yayin da 'yan bindiga suka bude masa mota a cikin motarsa kirar Marsandi.

A ranar 3 ga watan Fabrairu na shekarar 1976, marigayi Murtala ya samar da jihohi 7 wadanda suka hadar da; Bauchi, Benue, Borno, Imo, Niger, Ogun da kuma jihar Ondo. Har yanzu takardar Naira ashirin ta kudin Najeriya ta na dauke da hoton Marigayin.

5. Gen Olusegun Obasanjo (February 13, 1976 – October 1, 1979)

Gen Olusegun Obasanjo (February 13, 1976 – October 1, 1979)
Gen Olusegun Obasanjo (February 13, 1976 – October 1, 1979)

Janar Olusegun Obasanjo shine mutum na farko da ya shugabanci Najeriya wanda ya fito daga yankin Yammacin kasar nan, kuma an haifi a ranar 3 ga watan Mayu na shekarar 1937 a birnin Abeokuta dake jihar Ogun. Ya mulki kasar nan tun daga ranar 13 ga watan Fabrairu na shekarar 1976 zuwa ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1979, wato dai ya samu shekaru akalla uku akan kujerar mulki.

Obasanji ya mulki kasar nan a karo biyu na mulkin soja da na farar hula. Shine shugaban kasa da ya dawo da demukuradiyya Najeriya a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1979, inda ya yi murabus kuma ya danka mulkin kasar nan a hannun Alhaji Shehu Shagari.

6. Alhaji Shehu Shagari (October 1, 1979 – December 31, 1983)

Alhaji Shehu Shagari (October 1, 1979 – December 31, 1983)
Alhaji Shehu Shagari (October 1, 1979 – December 31, 1983)

An haifi Alhaji Shehu Shagari a ranar 25 ga watan Fabrairu na shekarar 1925, kuma shine shugaban kasa na farar huka na farko a kasar kafin Manjo Janar Muhammadu Buhari ya kwaci mulki a hannunsa a ranar 31 ga watan Dasumba na shekarar 1983.

Shagari shine shugaban kasar da ya kammala ginin matatar man fetur ta jihar Kaduna, tare da samar da kamfanin kera karfi guda uku dake Ajaokuta, cikin shekaru hudu da ya shugabanci kasar nan, tun daga ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1979 zuwa 31 ga watan Dasumba na shekarar 1983.

KARANTA KUMA: Allah wadaran naka ya lalace - Jibrin ga majalisar wakilai

7. Maj Gen Muhammadu Buhari (December 31, 1983 – August 27, 1985)

Maj Gen Muhammadu Buhari (December 31, 1983 – August 27, 1985)
Maj Gen Muhammadu Buhari (December 31, 1983 – August 27, 1985)

Manjo janar Muhammadu Buhari ya zo duniya ne a ranar 17 ga watan Dasumba na shekarar 1942 kuma an haife shi ne garin Daura ke jihar Katsina.

Sakamakon juyin mulki da ya yiwa Alhaji Shehu Shagari a ranar 31 ga watan Dasumba na shekarar 1983 ya zamzo shugaban kasar nan har zuwa 27 ga watan Agusta na shekarar 1985 inda Janar Babangida shi ma ya yi masa juyin mulki.

Buhari shine shugaban kasa na farko da ya fara yakar cin hanci da rashawa, inda ya tanadar da matakai kwarara da kuma dokoki na kawar da cin hancin hanci da rashawa tare da duk wata rashin da'a ko karya doka a kasar nan.

8. Gen Ibrahim Babangida (August 27, 1985 – August 26, 1993)

Gen Ibrahim Babangida (August 27, 1985 – August 26, 1993)
Gen Ibrahim Babangida (August 27, 1985 – August 26, 1993)

Haifaffen garin Minna na jihar Neja a ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 1941. A cikin shekaru takwas da ya shafe yana mulkin kasar nan, ya samar da jihohi 11 na kasar nan wadanda suka hadar da; Akwa Ibom, Katsina, Abia, Enugu, Delta, Jigawa, Kebbi, Osun, Kogi, Taraba da kuma Yobe.

Sakamakon nauyin shugabanci da ya ishe shi, ya yi murabus a ranar 26 ga watan Agusta na shekarar 1993 inda ya baiwa Ernest Shonekan ragamar mulkin kasar nan.

9. Ernest Shonekan (August 26, 1993 –November 17, 1993)

Ernest Shonekan (August 26, 1993 –November 17, 1993)
Ernest Shonekan (August 26, 1993 –November 17, 1993)

Ernest Shonekan ya shugabanci kasar nan cikin abinda bai wuci watanni uku ba, domin kuwa ya hau kujerar shugabanci a ranar 26 ga watan Agusta na shekarar 1993 kuma ya ajiye aiki a ranar 17 ga watan Nuwamba na shekarar.

An haifi shi a ranar 9 ga watan Mayu na shekarar 1936, yayin da shima ganin ba zai iya ba da kuma tursasawa ya baiwa Janar Sani Abacha akalar mulkin.

10. Gen Sani Abacha (November 17, 1993 – June 8, 1998)

Gen Sani Abacha (November 17, 1993 – June 8, 1998)
Gen Sani Abacha (November 17, 1993 – June 8, 1998)

An haifi Janar Sani Abacha a ranar 20 ga watan Satumba na shekarar 1943, kuma ya shugabanci kasar nan tun daga ranar 7 ga watan Nuwamba na shekarar 1993 zuwa ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 1998, inda ya gamu da ajalinsa.

Akwai jita-jitar cewa babu shugaban kasar da yayi almundahanarsa domin kuwa ana cewa gwamnati uku bayansa ba su iya karbo dukiyar da ya yiwa wawaso ba.

11. Gen Abdulsalami Abubakar (June 8, 1998 – May 29, 1999)

Gen Abdulsalami Abubakar (June 8, 1998 – May 29, 1999)
Gen Abdulsalami Abubakar (June 8, 1998 – May 29, 1999)

Sakamakon rasuwar Janar Abacha, Janar Abdulsalami Abubakar ya karbi jagorancin kasar nan a ranar 8 ga watan Yuni na shekarar 1998 zuwa 29 ga watan Mayu na shekarar 1999.

An haifi Abdulsalami a ranar 13 ga watan Yuni na shekarar 1942. A yayin karba mulkin kasar nan, ya sha alwashin maido da demukuradiyya kasar kuma ya cika alakawarinsa har aka gudanar da zabe a ranar kuma ya mika shugabancin kasar nan ga Olusegun Obasanjo a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999.

KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ba zan yi murabus ba - Mugabe

11. Chief Olusegun Obasanjo (May 29, 1999 – May 29, 2007)

Chief Olusegun Obasanjo (May 29, 1999 – May 29, 2007)
Chief Olusegun Obasanjo (May 29, 1999 – May 29, 2007)

Cif Olusegun Obasanjo ya dawo mulkin kasar a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 1999 zuwa ranar 29 na watan Mayu a shekarar 2007 a karo na biyu, amma a farar hula sakamakon wanzuwar demukuradiyya.

Obasanjo ne ya yi sanadiyar rushewar basussuka da ake bin kasar nan inda tsohuwar ministan Kudi Okonja Iweala tayi ruwa da tsaki a lokacin. Ya kuma kafa hukumar EFCC domin ladabtar da masu cin hanci da rashawa a kasar nan.

12. Umaru Musa Yar’Adua (May 29 2007 – May 5 2010)

Umaru Musa Yar’Adua (May 29 2007 – May 5 2010)
Umaru Musa Yar’Adua (May 29 2007 – May 5 2010)

Bayan saukar Obasanjo daga shugabanci, Umaru Musa Yar'Adua ya karbi ragamar shugabancin kasar nan a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2007 zuwa 5 ga watan Mayu na shekarar 2010, inda ajali ya yi halinsa sakamakon rashin lafiya wanda yayi shekaru uku kacal akan kujerar mulki.

An haifi Yar'Adua a ranar 16 ga watan Agusta na shekarar 1951 a jihar Katsina.

13. Goodluck Ebele Jonathan (May 6, 2010 – May 28, 2015)

Goodluck Ebele Jonathan (May 6, 2010 – May 28, 2015)
Goodluck Ebele Jonathan (May 6, 2010 – May 28, 2015)

Sakamakon shudewar Yar'Adua, Goodluck Ebele Jonathan ya karbi ragamar shugabanci kasar nan tun daga ranar 6 ga watan Mayu na shekarar 2010 zuwa 28 ga watan Mayu na shekarar 2015.

Mahaifar Jonathan ita ce jihar Bayelsa, kuma an haifi shi a ranar 20 ga watan Nuwamba na shekarar 1957, inda bayan ya kammala shugabancin da ya yi gado a matsayinsa na mataimakin shugaban kasa na lokacin Yar'Adua, ya kuma bayyana ra'ayinsa na tsayawa takara inda ya yi nasara kuma ya cigaba da shugabantar kasar.

14. Muhammadu Buhari (May 29, 2015 har zuwa yanzu)

Muhammadu Buhari (May 29, 2015 har zuwa yanzu)
Muhammadu Buhari (May 29, 2015 har zuwa yanzu)

Bayan fafutikar neman kujerar shugabancin kasar nan a shekarun 2003, 2007 da kuma 2011, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi nasarar lashe zaben shekarar 2015 a karo na hudu kenan na neman shugabancin.

Ya karbi shugabancin kasar nan a ranar 29 watan Mayu na shekarar 2015. Shine shugaban kasa na biyu da yayi mulki a farar hula da kuma mulkin soja bayan Obasanjo, wanda a yanzu ana sa ran zai sake tsayawa takara a zaben 2019 mai gabatowa.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel