Hadarin jirgin ruwa mai muni yaci mutane 17 yan kasuwa a jihar Kebbi

Hadarin jirgin ruwa mai muni yaci mutane 17 yan kasuwa a jihar Kebbi

Jaridar Rariya ta dauko wnai rahoton hadarin jirgin ruwa mai muni daya faru a kauyen Garin Alhaji Ila cake cikin garin Yawurin jihar Kebbi, na jihar Kebbi.

Wannan hatsari ya faru ne yayin da wani kwale kwale mai dauke da sama da mutane 50 ya kifa, bayan daya bigi wani katafaren ice, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA:

Dukan iccen keda wuya, sai jirgin ruwan ya dare gida biyu, hakan ya sanya jirgin nutsewa, inda mutane goma sha bakwai suka ce ga garinku nan, sa’annan mutane uku ba’a gansu ba sama ko kasa.

Hadarin jirgin ruwa mai muni yaci mutane 17 yan kasuwa a jihar Kebbi
Hadarin jirgin ruwa

A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Yawuri, Musa Muhammad Yawuri ya bayyana alhininsa da faruwar wannan mummunan lamari, inda tare da kansilolinsa suka kai ziyarar ta’aziyya zuwa inda lamarin ya auku.

A yayin ziyarar tasa, shugaban karamar hukumar ya bada umarnin a cigaba da neman sauran jama’a da ruwan yayi awon gaba dasu, sa’annan ya bada umarnina a garzaya da sauran gawawwakin zuwa babban Asibitin Yawuri.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

We need to understand the Biafra objective

Asali: Legit.ng

Online view pixel