Najeriya zata shiga cikin halin Kakani-kayi idan har bata samar da tattalin arzikin da ba na man fetur ba - Ezekwesili

Najeriya zata shiga cikin halin Kakani-kayi idan har bata samar da tattalin arzikin da ba na man fetur ba - Ezekwesili

- Tsohuwar Ministan Ilimi wato Obiageli Ezekwesili ta yi kira da a bunkasa tattalin arzikin Najeriya barin man fetur

- Ta ce idan har ba'a dau mataki ba toh nan gaba kadan Kasar zata shiga halin ni 'ya su

- Ta zargi Injiniyoyin Najeriya da taimakawa wurin dankwafar da kasan

Tsohuwar Ministar Ilimi wato Obiageli Ezekwesili ta ce Najeriya zata shiga cikin halin Kakaniya-kayi idan har bata samar da tattalin arzikin da ba man fetur ba. Ta ce nan gaba kadan kasar zata rinka kwankwadar man fetur din nata da kanta idan har ta ci gaba da dogara da shi.

Tshohuwar ministar ta yi wannan bayani ne a wani taron Kungiyar Injiniyoyin Tsarin-Gini da aka yi a Abuja. Ta ce tuni sauran kasashe masu samar da man fetur suka bunkasa tattalin arzkin su barin man fetur amma banda Najeriya.

Najeriya zata shiga cikin halin Kakaniya-kayi idan har bata samar da tattalin arzikin da ba man fetur ba- Ezekwesili

Ezekwesili

A jawabin da ta gabatar mai taken, ''Yaki da cin hanci da rashawa, rawar da Injiniyoyi za su taka'', ta zargi Injiniyoyi da taimkawa wajen bunkasa cin hanci da rashawa da ta addabi kasar. Ta ce dole ne Injiniyoyi su tashi tsaye don bada na su gudummuwar.

DUBA WANNAN: Hukumar EFCC ta sake waiwayar INEC

Idan mai karatu bai manta ba Naij.com ta kawo maku yadda Ezekwesili ta kushe jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatar a ranar zagayowar 'yancin kan Najeriya.

Ta ce jawabin na shugaban kasa mai iya kawo rabuwar kai ne kuma ba mai bada kwarin gwiwa bane.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Kaduna za ta gyara dokar hana shan barasa a jihar

Gwamnatin Kaduna za ta gyara dokar hana shan barasa a jihar

Gwamnatin Kaduna za ta gyara dokar hana shan barasa a jihar
NAIJ.com
Mailfire view pixel