Za a mayar da asibitin fadar shugaban kasa na kudi

Za a mayar da asibitin fadar shugaban kasa na kudi

- Asibitin fadar shugaban kasa zai koma na kudi

- Wasu sun koka kan cewa ba a samar da magunguna ga marasa lafiya a asibitin

- Asibitin fadar shugaban kasa ba a biyan anini idan za a ga likita

Manajan asibitin da ke fadar shugaban kasa ya shaida cewa za a maida asibitin fadar wanda da ake gudanar wa da marasa lafiya aikin kyauta na kudi don samar da ingataccen aiki ga marasa lafiya.

Famanen Sakatare, Jalal Arabi ne ya shaida hakan a ranar laraba yayin da yake maida wani martani a wani rahoto da ke cewa ana karancin magani a asibitin da kuma yadda yanayin asibitin ke ciki.

Za a mayar da asibitin fadar shugaban kasa na kudi

Za a mayar da asibitin fadar shugaban kasa na kudi

Daga wata majiya kuwa Naij.com ta sami rahoton yadda wasu suke kuka a kan yanayin da asibitin yake ciki, wasu suna kuka da cewa babu magani a asibitin, tun a watan Afrilu rabon da a kai magunguna asibitin.

A shafin Instagram na Zahra Buhari kuwa, ‘yar gidan shugaban kasar ta koka a kan yadda yanayin asibitin yake.

Duk da haka kuwa, Mista Arabi ya fitar da sanarwa da sa hannun Atta Esa mataimakin mai yada labarai a asibitin ya shaida yadda asibitn shi kadai ne a fadin Abuja da marasa lafiya basa biyan ko sisi kafin su ga likita.

A asibitocin gwamnati, marasa lafiya sai sun biya kudin ganin likita, da na magani da gwaje-gwaje sabanin hakan kuwa a na fadar shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Marasa lafiya a asibitin fadar shugaban kasa sun koka da karancin magani

Sakataren ya shaida yanzu yadda kowa zai dinga bin tsari a ganin likita, domin kuwa ba a biyan ko sisi sannan gwamnatin tana kashe makudan kudi wajen tabbatar da ingatattun kayan aiki a asibtin.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
A kori Buhari: Kwankwaso ya naɗa Buba Galadima shugabam yaƙin neman zaɓensa a takarar shugaban ƙasa

A kori Buhari: Kwankwaso ya naɗa Buba Galadima shugabam yaƙin neman zaɓensa a takarar shugaban ƙasa

A kori Buhari: Kwankwaso ya naɗa Buba Galadima shugabam yaƙin neman zaɓensa a takarar shugaban ƙasa
NAIJ.com
Mailfire view pixel