Amfani 7 na ruwan albasa wajen gyaran gashi

Amfani 7 na ruwan albasa wajen gyaran gashi

Sakamakon tsawon lokaci da gasu ke dauka waje taruwa, akwai nau'ukan kalubale da mafi yawan mutane ka fuskanta wajen kulawa da gasun su. Legit.ng ta kawo muku jerin hanyoyi na kulawa da gasu ta hanyar yin amfani da ruwan albasa sanadiyar bincike da ya fayyace sunadarai ma su alfanu ga gasu musamman na ka.

Yin amfani da ruwan albasa yana matukar taimakawa wajen inganta koshin lafiyar gasu, tare da yaye wasu cututtukan gasu da kai ya bayyana a gasun.

Ga jerin amfani 5 na ruwan albasa wajen inganta koshin lafiyar gasu.

1. Amfani wajen inganta koshin lafiya da yalwa tare da habaka fitowar gasu, sanadiyar taimakon sunadarin enzyme mai tallafawa wajen narkewar kwayoyin hydrogen peroxide masu inganta lafiyar gasu.

Amfani 5 na ruwan albasa wajen gyaran gashi
Amfani 5 na ruwan albasa wajen gyaran gashi

2. Yana taimakawa wajen inganta kwayoyin follicle na cikin gasu wadanda suke kunshe da sunadarin Sulfur. Matsayin Sulfur tamkar taki ne a gona, ya na kuma hana sirancewar gasu da hana karyewar su

3. Sunadaran antioxidants suna tallafawa wajen hana fitowar furfurar gasu da wuri.

KARANTA KUMA: Buhari: Akwai rikon sakainar kashi da Baru yake yiwa NNPC - Kachikwu

4. A sakamakon sunadaran antibacterial na cikin ruwan albasa, su na taimakawa jijiyoyin gasu wajen kubuta daga cututtuka musamman amosani tare da inganta koshin lafiyar su.

5. Yana kuma inganta zagayawar jini a cikin jijiyin gasu ta hanyar inganta kwayoyin follicle na cikin ka.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel