Wata sabuwar cuta makamaciyar kyanda ta barke a jihar Bayelsa, an killace mutane 10 tare da likita guda

Wata sabuwar cuta makamaciyar kyanda ta barke a jihar Bayelsa, an killace mutane 10 tare da likita guda

Hankula da dama sun tashi tare da durar ruwa a cikin al'ummar jihar Bayelsa sakamakon barkewar wata sabuwar cuta makamanciyar kyanda da farankama mai sunan monkeypox (Cutar kuraje da aka samu daga biri).

A cewar kungiyar lafiya ta duniya (World Health Organisation, WHO), wannan cuta tana fitowa ne daga wasu yankunan tsakiyar Afirka ta Afirka ta Yamma, inda kungiyar ta ce wannan cuta ta na kamanceceniya da cutar kyanda sai dai kyanda ba ta kisa.

Legit.ng ta samu rahoton cewa, akwai mutane goma da likita guda wanda suka kamu da wannan cuta kuma an killace su a wani bangare na asibitin koyarwa na Neja Delta dake garin Okolobiri na karamar hukumar Yenagoa.

Wata sabuwar cuta makamanciyar kyanda ta barke a jihar Bayelsa, an killace mutane 10 tare da likita guda
Wata sabuwar cuta makamanciyar kyanda ta barke a jihar Bayelsa, an killace mutane 10 tare da likita guda

Kwamishinan lafiya na jihar ta Bayelsa Farfesa Ebitimitula Etebu, ya tabbatar da faruwar wannan abu inda ya ce akwai kimanin mutane 49 da cibiyar lafiya take bibiya da ake zargin sun kamu da wannan cuta.

KARANTA KUMA: Cibiyoyin Jakadancin Najeriya a kasashen ketare su na ganin takansu - Akpabio

Ya kuma bayyana cewa kwayoyin cutar farankama da kyanda ke haddasa wannan cuta sakamakon bincike da aka gudanar a baya bayan cutar ta barke a Jamhuriyyar Congo.

Masana kiwon lafiya na kungiyar lafiya ta duniya sun dukufa wajen binciken wannan cuta a cibiyarsu dake Dakar a kasar Senegal.

Etebu ya kara da cewa, an fara samun wannan cuta ne a jikin biri kuma ana iya samun ta naman dawa irinsu bushiya, gafiya da kuma bodari. Ya kuma ce wannan cuta ta na sanyawa masu dauke da ita ciwon kai, zazzabi, ciwon baya da kuma fesowar kuraje a gaba daya sassa na jiki.

Domin shawara ko bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel