Buhari na karkatar da kudin NNPC domin yakin neman zaben 2019 - Fani Kayode

Buhari na karkatar da kudin NNPC domin yakin neman zaben 2019 - Fani Kayode

- Fani Kayode ya zargi Shugaban Kasa Muhammadu Bubari da satan kudin NNPC don takaran sa na Shugabancin Kasa a 2019

- Ya yi ikirarin babu inda Buhari zai samu kudin kamfen sai ta hakan

A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta fitar da mutane da zasu binciki Babban Manaja na Ma'aikatar Matatan Man Fetur wato NNPC , Dakta Maikanti Baru, bisa ga zargin sa da Ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya yi a wata rubutacciyar kara da ya aikawa Buhari.

Buhari na karkatar da kudin NNPC domin yakin neman zaben 2019: Fani Kayode

Buhari na karkatar da kudin NNPC domin yakin neman zaben 2019: Fani Kayode

Sakamakon haka sai tsohon Ministan Hukumar Tukin Jirgin sama wato Fani Kayode, a shafin sa na tuwita ya zargi shugaba Buhari da 'yan koran sa da satan kudin don tsayawa takaran sa na shugabancin Kasa.

DUBA WANNAN: Najeriya zata shiga cikin halin Kakani-kayi idan har bata samar da tattalin arzikin da ba na man fetur ba - Ezekwesili

Ga yadda ya rubuta a shafin nasa, ''Ibe Kachikwu bai amince da yadda Muhammadu Buhari da 'yan koran sa basu dauki washe kudi dala biliyan 26 daga NNPC a bakin komai ba.''

Ya ci gaba da cewa, ''Idan ba a nan ba ina ake tsammanin zai samu kudin da zai tsaya takara a shekarar 2019?''

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
Hukumar NAPTIP ta cafke wata mata da ta kona kanwar mijinta da tafasashshen ruwa

Hukumar NAPTIP ta cafke wata mata da ta kona kanwar mijinta da tafasashshen ruwa

Hukumar NAPTIP ta cafke wata mata da ta kona kanwar mijinta da tafasashshen ruwa
NAIJ.com
Mailfire view pixel