Ba makawa, Gbenga Daniel ne shugaban jam’iyyar PDP mai jiran gado – Inji IBB

Ba makawa, Gbenga Daniel ne shugaban jam’iyyar PDP mai jiran gado – Inji IBB

- Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nuna goyon bayansa ga OGD

- Otunba Gbenga Daniel, OGD, na takarar shugaban jam'iyyar PDP

Tsohon shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida ya nuna goyon bayansa ga tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel a matsayin dan takarar shugaban jam’iyyar PDP.

Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da tsohon gwamnan ya fitar ta bakin wakilansa cewa IBB ya goyi bayan Gbenga ne a gidansa dake Minna, yayin wata ziyara da Gbengan ya kai masa.

KU KARANTA: Jagwal: Wani mutumi ya ɗauki alhakin yi ma Uwa da Ýarta ciki a lokaci ɗaya

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Gbenga Daniel na fadin ya kai ziyarar ne ga IBB domin tattaunawa da shi game da muradinsa na yin takarar shugaban PDP, inda yace babu wani dan siyasa mai hankali da zai nemi wannan mukami ba tare da ya nemi sa albarka su IBB ba.

Ba makawa, Gbenga Daniel ne shugaban jam’iyyar PDP mai jiran gado – Inji IBB

Gbenga Daniel da IBB

Dayake nasa jawabin, IBB ya bayyana jin dadinsa da takarar Gbenga Daniel, inda yace “Nayi matukar farin ciki lokacin dana ji kana kokarin sadaukar da kanka ka tsaya takara, dama lokaci yayi da za’a ba matashi daman tsayawa takara.

Ba makawa, Gbenga Daniel ne shugaban jam’iyyar PDP mai jiran gado – Inji IBB

Traon

“Na san OGD sosai, kuma na san zai kai jam’iyyar PDP ga gaci, ina goyon bayanka, ina sa ran kai ne shugabana a jam’iyyance mai jiran gado.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36
NAIJ.com
Mailfire view pixel