Shugaba Buhari ya kusa kamuwa da hawan jini - Inji Amaechi

Shugaba Buhari ya kusa kamuwa da hawan jini - Inji Amaechi

Babban ministan harkokin sufuri na Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari kuma mamba a majalisar zartarwar kasa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa saura kadan jinin shugaba Buhari ya hau saboda yana da matukar son harkokin sufuri su habaka.

Ministan dai ya bayyana cewa matukar sha'awar da shugaban yake yi wa harkar sufuri ne ma yasa ya aika aka kira shi domin ya zo yayi masa karin haske game da inda aka kwana a bisa maganar ayyukan hanyoyin jiragen kasa da Gwamnatin ta tsira.

Shugaba Buhari ya kusa kamuwa da hawan jini - Inji Amaechi

Shugaba Buhari ya kusa kamuwa da hawan jini - Inji Amaechi

KU KARANTA: Yakin neman zaben Atiku a 2019 ya kankama

NAIJ.com ta samu da cewa Minista Amaechi da ke zaman tsohon Gwamnan jihar Ribas yayi wannan jawabin ne ga manema labarai na fadar shugaban kasar jim kadan bayan ya fito daga ganawar sirrin da yayi da shugaban kasar.

Amaechi ya bayyana cewa kiran da yayi masa haka ma dai ya bashi damar ya yi masa gamsasshen bayani akan inda aka kwana game da shinfida hanyar jirgin kasa daga Ribas din zuwa Borno.

Source: Hausa.naij.com

Related news
Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36
NAIJ.com
Mailfire view pixel