Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Borno ya yanke jiki ya fadi matacce a masaukin sa

Yanzu-yanzu: Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Borno ya yanke jiki ya fadi matacce a masaukin sa

- Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Borno ya yanke jiki ya fadi matacce a dakin hotal din sa

- Sani Datti ya tabbatar da mutuwarsa

- Har yanzu ba a gano musababbin mutuwarsa ba

An tabbatar da mutuwar shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Borno, Mista Abdulsalam Badamasi, bayan da yanke jiki ya fadi a dakin hotal din da yake.

Shugaban Hukumar NEMA na arewa maso gabas ya mutu a Otal a Maiduguri

Shugaban Hukumar NEMA na arewa maso gabas ya mutu a Otal a Maiduguri

Jami'in hukumar mai yada labarai, Sani Datti, ya tabbatar da mutuwar shugaban a wata hirar wayar tarho da yayi da gidan jaridar Daily trust, sannan ya bayyana cewar hukumar zata fitar da sako a rubuce.

Sani ya ce "Eh, da gaske ne ya mutu, bayan da ya yanke jiki ya fadi a dakin hotal din da yake da safiyar yau juma'a".

DUBA WANNAN: Gwamnan jihar Akwa Ibom ya bawa Super Eagles kyautar kudi $50,000

Kafin a dawo da shi jihar Borno a watan da ya gabata, Mista Badamasi, ya kasance shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa a jihar Filato.

Zamu kawo maku karin bayani...ku kasance tare da hausa.naij.com

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36
NAIJ.com
Mailfire view pixel