World Cup: Najeriya ta na da babban wasa da kasar Zambiya

World Cup: Najeriya ta na da babban wasa da kasar Zambiya

– Kungiyar Kwallon Najeriya za ta kara da Kasar Zambia

– Super Eagles ta doke 'Yan Chipolopolo kwanaki da ci 2-1

– Idan Najeriya ta samu nasara za ta je Gasar kofin Duniya

A karshen wannan makon Kungiyar Super Eagles za su buga wani babban wasa da kasar Zambia domin zuwa gasan kofin Duniya.

World Cup: Najeriya ta na da babban wasa da kasar Zambiya

'Yan wasan Super Eagles a wasan su da Zambia

Kungiyar Kwallon Najeriya za su kara da takwarar su ta Kasar Zambia a gobe a filin wasa na Godwil Akpabio da ke Garin Uyo. A karon baya Super Eagles ta doke kasar Zambia har gida da ci 2-1 wanda Alex Iwobi da Kelechi Iheanacho suka jefa kwallayen.

KU KARANTA: Gwamnatin Shugaba Buhari ta bada wasu ayyuka

Idan Najeriya ta samu nasara tana da ran zuwa kasar Rasha domin gasar cin kofin Duniya a shekara mai zuwa. Kyaftin din Najeriya Mikel Obi yace ba za su ce komai ba a wasan sai an buga. Najeriya dai ce gaba a teburin ta inda Kasar Zambia ke bi ma ta.

Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta samu zuwa Gasar World Cup na 6 idan har ta doke takwarar ta Kasar Zambia a wasan zuwan cin kofin na gobe da yamma a Najeriya. Shugaban Kasa Buhari ya tura Ministan ayyuka Babatunde Fashola ya wakilce sa a wasan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel