Karya ne Buhari bai samar da tsaro ba a Borno - Buba Galadima

Karya ne Buhari bai samar da tsaro ba a Borno - Buba Galadima

Fitaccen dan siyasar nan kuma jigo a jam'iyya mai mulki ta APC Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa shi bai yadda da karairayin da ake ta yi ba na cewa wai an samu zaman lafiya a Maiduguri don kuwa duk labarin kanzon kurege ne.

Injiniya Buba Galadima da a 'yan kwanakin nan sunan sa ke ta yawo a kafafen yada labarai na cikin gida Najeriya ya bayyana cewa har yanzu babu cikakken tsaro a jihar Borno kamar yadda ake ta yamadidi a cikin gari.

Karya ne Buhari bai samar da tsaro ba a Borno - Buba Galadima

Karya ne Buhari bai samar da tsaro ba a Borno - Buba Galadima

KU KARANTA: Ku karanta wani gari da maza ke shigar mata

NAIJ.com ta samu cewa shahararren dan siyasar ya kuma ce zai yadda da maganar samar da tsaron ne a jihar idan har mutane za su iya daukar mota su tuka daga duk inda suke su je wasu garuruwan dake a cikin jihar ta Borno irin su Baga da Chibok da dai sauran su.

A kwanan baya dai mai karatu zai iya tuna cewa Buba Galadima ya shaidawa majiyar mu ta BBC Hausa cewa idan da shine shugaban INEC da tuni ya wargaza jam'iyyar APC don kuwa ta karya sharuddan kafa ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Gwamnatin Kaduna za ta gyara dokar hana shan barasa a jihar

Gwamnatin Kaduna za ta gyara dokar hana shan barasa a jihar

Gwamnatin Kaduna za ta gyara dokar hana shan barasa a jihar
NAIJ.com
Mailfire view pixel