Dan wasan Super Eagles ya samu mukudan kyauta a wasan Zambia

Dan wasan Super Eagles ya samu mukudan kyauta a wasan Zambia

- Dan wasan Super Eagles ya samu lambar yabo a wasan jiya

- Shehu Abdullahi ne gwarzo a karawar Najeriya da Zambiya

- Kun ji Kungiyar Super Eagles ta samu zuwa Gasar World Cup

Mun samu labari cewa Dan wasan bayan Kungiyar Super Eagles ya tashi da kyauta iri-iri bayan Najeriya ta doke Zambia jiya.

Dan wasan Super Eagles ya samu mukudan kyauta a wasan Zambia

Kyaftin din Kungiyar Super Eagles Mikel Obi

Dan wasan bayan Najeriya Shehu Abdullahi ne dai gwarzon wasan na jiya a sa’ilin da aka gwabza da Kasar Zambia. A sanadiyyar haka ne ma aka ba shi kyautar kudi har Naira Miliyan guda (N1, 000,000) Inji Jaridar Punch.

KU KARANTA: Najeriya ta samu zuwa Gasar World Cup

Dan wasan Kasar da ke bugawa Kungiyar Anorthosis yayi matukar kokari a jiya inda ya rike gidan sa ya kuma hana ‘yan bayan Zambia sakat. Shehu Abdullahi ne ma dai ya kawowa Alex Iwobi kwallon da ya zuba a raga a minti na 75 a wasan.

Idan ba ku manta ba Shugaban Kasa Buhari yayi magana game da nasarar da Super Eagles ta samu zuwa Gasar cin kofin Duniya da za ayi a Kasar Rasha shekara mai zuwa inda yace 'Yan wasan sun nuna bajinta da kokarin gaske.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36
NAIJ.com
Mailfire view pixel