Gwamnatin jihar Bauchi zata bunkasa ilimin boko a makarantun sakandire

Gwamnatin jihar Bauchi zata bunkasa ilimin boko a makarantun sakandire

- Gwamnatin jihar Bauchi zata bunkasa ilimin boko a makarantun firamare da sakandire na jihar

- Kungiyoyin samar da ingataccen ilimi zasu tallafawa gwamnatin jihar

- Makarantun gwamnati suna bukatar malaman da zasu ba dalibai nagartaccen ilimi

Gwamnatin jihar Bauchi zata bunkasa ilimin boko a makarantun sakandire da firamare na jihar tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu bada tallafi a ilimin boko.

Sabo Muhammad, mai bawa gwamnan jihar shawara akan hakokin ilimi ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar bazata a makarantar sakandaren kimiyya a cikin makon nan.

Gwamnatin Bauchi zata bunkasa ilimin boko

Gwamnatin Bauchi zata bunkasa ilimin boko

Malam Muhammad ya shaida cewa gwamnatin jihar kadai bazata iya farfado da darajar ilimin jihar ba, amma tare da hadin gwiwar wasu kafofin za'a samu a farfado da ilimin saboda daliban makarantun gwamnati su sami ingataccen ilimi.

Ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar zata yi iya bakin kokarin ta wajen samar da ingataccen ilimi ga daliban makaranta.

DUBA WANNAN: Sarki Salman na Saudiyya ya gana da Shugaba Vladimir Putin; ya ci alwashin kawo karshen gallazawa Falasdinawa

Ya yi kira ga malaman makarantar sakandire na jihar da su jajirce wajen bawa daliban nagartaccen ilimi. Ya kuma yaba da yadda yaga malaman suna kokari wajen koyar da daliban ilimi mai anfani.

Muhammad Bala Wunty, mai na ofishin ilimi na jihar yayi godiya wa gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar a bisa gyare-gayren da yayiwa ofishin nasu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naij.com

Related news
Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36
NAIJ.com
Mailfire view pixel