Gwamnatin Buhari ta saba alkawarin da ta yiwa 'yan Najeriya – Inji kungiyar matasan Arewa

Gwamnatin Buhari ta saba alkawarin da ta yiwa 'yan Najeriya – Inji kungiyar matasan Arewa

- Kungiyar matasan arewa ta ce gwamnatin Buhari ta saba alkawarin da ta yiwa 'yan Najeriya

- Kungiyar ta ce mafi yawan 'yan Najeriya na fama da talauci da damuwa daban-daban

- Matasan sun koka cewa lokaci na canji yanzu ne kafin ya yi latti

Kungiyar matasa na Arewa, AYF, ta koka a kan cewa shugaba Muhammadu Buhari da tawagarsa sun kasa da tsammanin 'yan Najeriya.

Shugaban kungiyar AYF, Gambo Ibrahim Gujungu, a cikin wata sanarwa a Kaduna a ranar Lahadi, 8 ga watan Oktoba ya ce, "Matasan sun kuma bukaci shugabba Buhari ya yi gyaran bawu a majalisar ministoci saboda wadanda aka sa ran su taimaka wa shugaban a cikin sauyin sauye-sauye sun gaza a aiwatar da ayyukansu."

"Yanayin da mafi yawan 'yan Najeriya ke fama da talauci da damuwa daban-daban, inda mutane ba za su iya ci abinci sau biyu ba a rana balentana sau uku a rana, wannan abin damuwa ga 'yan Najeriya”.

Gwamnatin Buhari ta saba alkawarin da ta yiwa 'yan Najeriya – Inji kungiyar matasan Arewa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

"Lokaci na canji yanzu ne kafin ya yi latti".

KU KARANTA: Ku bar ganin laifin mukarraban Buhari, laifin sa ne - Dakta Aminu Gamawa

"Saboda haka muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari nan da nan ya fara yin gyaran bawu a majalisar ministoci don ya kawo 'yan Najeriya masu iyawa waɗanda za su iya taimaka masa wajen canja halin da al’ummar kasar ke ciki yanzu”.

Kungiyar ta ci gaba da cewa : "A matsayin mu na kungiyar matasan arewacin Najeriya da masu damuwa wajen inganta rayuwar matasa a Najeriya, mun damu da halin da ake ciki a kasar nan”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel