Sauya fasalin kasa: Dole a maida mana Juma'a ranar hutu - Inji wata kungiyar musulmai

Sauya fasalin kasa: Dole a maida mana Juma'a ranar hutu - Inji wata kungiyar musulmai

Wata kungiyar yan uwa musulmai dake rajin kare hakkin mabiya addinin islama a Najeriya mai suna Muslim Rights Concern (MURIC) a turance ta gabatar da nata bukatun ga kwamitin da jam'iyyar APC ta kafa da zai yi duba akan yiwuwar sake fasalin kasar nan.

Kungiyar karkashin jagorancin Farfesa Ishaq Akintola ta bayyana wa manema labarai mukatun nata ne a yau litinin a cikin wata sanarwar da ta fitar game da lamarin.

Sauya fasalin kasa: Dole a maida mana Juma'a ranar hutu - Inji wata kungiyar musulmai

Sauya fasalin kasa: Dole a maida mana Juma'a ranar hutu - Inji wata kungiyar musulmai

KU KARANTA: Gwamnan Jigawa na fuskantar barazanar tsigewa

NAIJ.com ta samu dai cewa bukatun da kungiyar ta zayyana wa kwamitin na jam'iyyar APC sun hada da maida ranar Juma'a ta zama ranar hutu musamman ganin yadda ita ma ranar Lahadi ake hutawa sai kuma ita ma ranar daya ga watan Muharram din ko wace shekara ta zama ranar hutu kamar dai yadda Kiristoci ke yi.

Sauran bukatun na kungiyar kamar dai yadda suka zayyana sun hada da tabbatar tare kuma da hukumantar da auren musulmai a hukumance kamar yadda kiristoci ke yi haka ma kuma a rika barin matan musulmai dake aikin kaki a suna saka hijabi da dai sauran su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Karin albashi: Shugaban kungiyar kwadago yayi wa ma'aikatan kasar nan bushara

Karin albashi: Shugaban kungiyar kwadago yayi wa ma'aikatan kasar nan bushara

Karin albashi: Shugaban kungiyar kwadago yayi wa ma'aikatan kasar nan bushara
NAIJ.com
Mailfire view pixel