Kamata yayi shugaban kasa ya rika yin wa'adin mulki 1 na shekara 5 ko 6 - Ekweremadu

Kamata yayi shugaban kasa ya rika yin wa'adin mulki 1 na shekara 5 ko 6 - Ekweremadu

Mataimakin shugaban majalisar dattijai kuma Sanata mai wakiltar jihar Enugu Sanata Ekweremadu ya bayar da shawarar cewa shugaban kasa ya rika yin wa'adin mulki daya kacal sai a kara yawan shekarun mulkin nasa zuwa shekaru 5 ko kuma 6.

A cewar sa, yin hakan zai taimaka gaya wajen kara karfafa siyasa da kuma samun karfi da lagwadar demokradiyya ga yan kasa.

Kamata yayi shugaban kasa ya rika yin wa'adin mulki 1 na shekara 5 ko 6 - Ekweremadu

Kamata yayi shugaban kasa ya rika yin wa'adin mulki 1 na shekara 5 ko 6 - Ekweremadu

KU KARANTA: Nadin Aisha Ahmad cin fuska ne ga musulmai

NAIJ.com ta samu dai cewa Sanata Ekweremadu yayi wannan tsokacin ne a yayin da yake gabatar da wata kasaida a wani taron da wata kungiyar da ba ta gwamnati ba mai mazauni a birnin New York Centre for Media and Peace Initiatives a turance.

Mataimakin shugaban majalisar dattijan Ekweremadu ya bayyana cewa wa'adin mulki dayan zai ma taimaka wa kasar wajen rage kashe kudaden gudanar da zabe duk bayan shekara hudu.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Saura kiris mu ci nasara game da karin kudin albashin ma'aikata

Saura kiris mu ci nasara game da karin kudin albashin ma'aikata

Karin albashi: Shugaban kungiyar kwadago yayi wa ma'aikatan kasar nan bushara
NAIJ.com
Mailfire view pixel