Daga Kannywood: Maryam Booth ta zazzaga ma Saurayinta kalaman Soyayya

Daga Kannywood: Maryam Booth ta zazzaga ma Saurayinta kalaman Soyayya

Fitacciyar jarumar Fina finan Kannywood Maryam Booth ta bayyana soyayyarta ga Sahibinta, wanda bata bayyana sunansa ba a shafinta na Instagram, inji rahoton Kannywood Scene.

Majiyar NAIJ.com ta shaida cewa Maryam Booth ta yi ma wannan Saurayi nata kalaman Soyayya ne yayin dayake bikin sake zagayowar ranar haihuwarsa a yau 10 ga watan Oktoba.

KU KARANTA: An sallami yan majalisa guda 2 daga majalisar dokokin jihar Sakkwato

Maryam ya bayyana Sahibin nata a matsayi wani ginshiki a rayuwarta, wanda ya sake bata damar kara yin soyayya bayan ta shiga matsala a soyayya a baya, sa’annan ta daura hoton tad a shi.

Daga Kannywood: Maryam Booth ta zazzaga ma Saurayinta kalaman Soyayya

Daga Kannywood: Maryam Booth da Saurayinta

“Ka shigo rayuwata a daidai lokacin da aka ci amanata a soyayya, kai ne wanda ka warkar cutar soyayya dake damuna, kuma ka nuna min yadda ake soyayyar gaske. Don haka nake taya ga murnan sake zagayowar ranar haihuwarka."

A wani labarin kuma, Maryam ta baiwa masoyanta hakuri, inda tace laifin daraktoci da furodusoshi ne yasa ba’a ganinta cikin fina finai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Gidan mawaki Fela, kalla a NAIJ.com Tv

Source: Hausa.naij.com

Related news
Saura kiris mu ci nasara game da karin kudin albashin ma'aikata

Saura kiris mu ci nasara game da karin kudin albashin ma'aikata

Karin albashi: Shugaban kungiyar kwadago yayi wa ma'aikatan kasar nan bushara
NAIJ.com
Mailfire view pixel