Barkewar gudawa ya kashe wasu a Kasar nan

Barkewar gudawa ya kashe wasu a Kasar nan

- Annobar Gudawa ta barke a wasu Jihohin kasar nan

- Cutar tayi sanadiyyar mutuwar mutane 8 a halin yanzu

- Wata cibiya da ke kula da cututtuka ta bayyana wannan

Mun samu rahoto mai ban takaici daga Jaridun Kasar nan na cewa barkewar gudawa ya kashe wasu a Najeriya kwanan nan.

Cutar gudawa ta hallaka jama'a a Najeriya

Cutar gudawa ta hallaka jama'a a Najeriya

Labari ya kai gare mu cewa wata cibiya da ke kula da cututtuka a Kasar nan ta bayyana cewa gudawa na cigaba da kashe mutane a Kasar nan inda akalla sama sa mutane 126 su ka mutu a sanadiyyar cutar na gudawa bana a Najeriya.

KU KARANTA: Za a hana saida jabun magunguna a Najeriya

Hukumar dillacin labarai na kasa NAN ta bayyana cewa mutane sama da 8,200 su ka kamu da cutar a Jihohi 8 na kasar wadanda su ka hada da Jihar Zamfara, Kwara, Borno, Lagos, Oyo, Kebbi, Kaduna da kuma Kano.

A yanzu haka dai an rasa mutane 8 a Kasar. Ko a kwanakin baya cutar ta kashe mutane a Yankin Kudancin Kaduna idan ba ku manta ba.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta rahoto cewa kusan mutane 9000 su ka mutu a sanadiyyar cutar gudawa a Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36

Buhari yayi umurnin hada tashar jirgin kasa zuwa manyan biranen jihohi 36
NAIJ.com
Mailfire view pixel