Farashin shinkafar Hausa ya sauko a kasuwannin garin Jalingo

Farashin shinkafar Hausa ya sauko a kasuwannin garin Jalingo

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito farashin shinkafar Hausa ta fadi warwas a kasuwannin garin Jalingon jihar Taraba, kamar yadda binciken ta ya nuna mata a ranar Laraba 11 ga watan Oktoba.

Majiyar Legit.ng ta zagaya kasuwannin Gadar Bobboji, Kasuwan Bera da kuma Kasuwan Mile Six, inda ta binciko farashin kwanun shinkafa akan naira 480 zuwa naira 550, wanda a satin biyu da suka gabata suke akan naira 650, zuwa 750.

KU KARANTA: Yan bindiga sun hallaka tsohon Sakataren gwamnatin jihar Filato

Shi kuwa buhun shinkafar Hausa wanda ake siyar da shi akan kudi naira N28,000 zuwa N30,000 a satin daya gabata, ya dawo Naira 23,000 zuwa N24,000.

Farashin shinkafar Hausa ya sauko a kasuwannin garin Jalingo
Shinkafar Hausa

Shugaban yan shinkafa na kasuwar Bobboji, Alhaji Nura Mohammed, ya danganta saukar farashin shinkafar da yawaitan shinkafar a kasuwa, sakamakon noman albarkar noma da aka samu.

Mohammed ya kara da cewa farashin ka iya cigaba da sauka, gabannin karatowar karshen shekara, matukar an ci gaba da samun sa akai akai a kasuwanni.

A wani labarin kuma, farashin shinkafar Turawa ta cigaba da hauhawa, inda ake siyar da kwanu daya akan kudi N1000, ba kamar yadda ake siyar da shi N950 a satin data gabata ba, yayin da ake siyar da buhunsa akan kudi N18,500 zuwa N19,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel