Legas: EFCC ta cafke wasu daraktoci 4 a kan zargin almubazzaranci

Legas: EFCC ta cafke wasu daraktoci 4 a kan zargin almubazzaranci

- Hukumar EFCC ta garkame wasu daraktoci 4 a kan zargin almubazzaranci da kudaden gwamnati

- Daraktocin sun ki amince da gayyatar hukumar EFCC

- Ana zargin su da almubazzaranci da fiye da naira miliyan 33

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a ranar Laraba, 11 ga watan Oktoba ta kama wasu daraktoci 4 na gidan wasan kwaikwayo ta kasa a Legas saboda zargin cin hanci da rashawa na makuddan kudade na gwamnati.

Majiyar NAIJ.com ta tabbatar da cewar an kama daraktocin 4 ciki har da mace, a ofishin su da ke Iganmu domin zargin cewa sun karkatar da wasu makuddan kudadin shiga.

A cewar majiyoyin, daga cikin kudaden gwamnati da ake zargi daraktocin da su sun hada da naira miliyan 24 na kudin haya da kamfanin Breweries ta biya da kuma naira miiyan 9 da aka biya don amfani da gidan wasan kwaikwayon kasa a lokacin bikin "Legas @ 50".

Legas: EFCC ta cafke wasu daraktoci 4 a kan zargin almubazzaranci

Hukumar EFCC

Rahotanni sun bayyana cewa, an tafi da daraktocin da al’amarin ta shafa bayan da suka ki amincewa da gayyatar EFCC.

KU KARANTA: EFCC ta bankado Naira Biliyan 2.1 a asusun mahaifiyar uwargidan Jonathan

Yayin da yake magana da taron masu zanga zanga a kan yaki da cin hanci da rashawa a ofishin, shugaban gidan wasan kwaikwayo na kasa ya yi alkawarin kawar da cin hanci da rashawa a ma'aikatar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Hotuna: Shugaba Buhari ya dira a kasar Taki domin halartar taron hadin kai

Hotuna: Shugaba Buhari ya dira a kasar Taki domin halartar taron hadin kai

Hotuna: Shugaba Buhari ya dira a kasar Taki domin halartar taron hadin kai
NAIJ.com
Mailfire view pixel