Wata Kotun Musulunci ta yi fatali da ƙarar da aka shigar da Sheikh Kabiru Gombe a Kano

Wata Kotun Musulunci ta yi fatali da ƙarar da aka shigar da Sheikh Kabiru Gombe a Kano

Wata shari’a data dauki jama’a a kotu shari’ar Musulunci dake jihar Kano, wanda ta hada da sanannen Malamin addinin Musulunci, Kabiru Gombe da kuma makwabcinsa ta zo karshe.

Idan ba’a manta ba, Legit.ng ta kawo muku rahoton sammaci da kotu ta kai ma Shehin Malamin daya gurfana a gabanta, sakamakon kara da wani makwabcinsa, Mu’awiyya Aminu Sagagi ya kai gabanta.

KU KARANTA: Mun Gode – Inji Jama’an garin Gwoza ga Sojojin Najeriya (Bidiyo)

Wannan kara da Sagagi ya kai, ya tattara ne da tagan shan iska na sabon gidan Shehin Malamin dake unguwar Sabuwar Gangu da aka gina, inda yace Taga yayi girma, kuma yayi zargin Malamin zai dinga lekan musu mata.

Wata Kotun Musulunci ta yi fatali da ƙarar da aka shigar da Sheikh Kabiru Gombe a Kano
Gidan Kabiru

Sai dai jaridar Rariya ta ruwaito bayan bayyanar shaidu daga bangaren mai kara, inda yace ai tuni Shehin Malamin ya sauya fasalin Tagan nasa, hakan ne yayi dalilin sallamar karar daga gaban kotun.

Shima a nasa hukuncin, Alkali Ibrahim Sarki Yola yace kotu ta gamsu da gyaran Shehin Malamin yayi, daga karshe ya umarce shi da kada ya sake bude Tagar a nan gaba.

Wata sabuwa kuma data taso daga bakin lauyan sheikh Kabiru Gombe, Ishaq Adam Ishaq yace babu wani abin da aka canza a gidan, yace ginin na nan yadda yake, ya kara da cewa sabanin akida ne kawai yasa Sagagi maka Shehin Malamin gaban kotu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel