Zidane da daf da doke tarihin da Guaradiola ya kafa a La Liga

Zidane da daf da doke tarihin da Guaradiola ya kafa a La Liga

Babban kocin kungiyar nan shahararra ta Real Madrid da ke a kasar Sifen watau Zineden Zidane na daf da karya karin wani tarihi da tsohon kocin na kungiyar Barcelona ya taba kafawa sadda yana kungiyar a shekarun baya.

Ranar Asabar ne dai ta karshen makon nan kungiyar ta Real Madrid za ta ziyarci kungiyar Getafe a gidan ta a cigaba da gasar ta La Liga wasan mako na 8 kuma idan har suka yi nasara a kan ta to zata zama kungiya ta farko kuma a karkashin mai horaswar Zidane da ta ci wasa 13 a jere ba a gidan ta ba.

Zidane da daf da doke tarihin da Guaradiola ya kafa a La Liga

Zidane da daf da doke tarihin da Guaradiola ya kafa a La Liga

KU KARANTA: Yan kunar bakin wake 4 sun mutu a Maiduguri

NAIJ.com ta samu dai cewa kungiyar a karkashin jagorancin Zidane ta doke Villarreal a ranar 26 ga watan biyu na shekarar 2016 ta kuma doke ta 3-2, tun daga wannan lokacin ta dunga cin wasannin ta na gasar ta La Liga da ta yi a waje.

Kungiyar da ta Real Madrid ta fara gasar wasan kwallon kafar a wannan kakar da kafar hagu bayan kungiyoyin Valencia da Levante da ma Betis suka kwaci maki biyar a kan Real Madrid din.

Amma duk da hakan kungiyar ta Real Madrid ta samu tayi nasarar doke Deportivo da Real Sociedad da Alaves da kuma Espanyol a wasannin da ta buga a waje.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naij.com

Related news
Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas

Wasu gwamnonin Najeriya 17 za su gana a ranar Litinin a Legas
NAIJ.com
Mailfire view pixel