Rikicin Filato: An binne mutum 27, Shugaba Buhari yace a dauki tsatsauran matakai akan lamarin

Rikicin Filato: An binne mutum 27, Shugaba Buhari yace a dauki tsatsauran matakai akan lamarin

- Buhari ya bayar da umurnin daukan mataki game da kashe-kashen, ya kuma mika ta'aziyar sa

- Kashe-kashen ya ki tsayawa duk da dokar takaita zirga-zirga da gwamnati ta saka

- Ana zargin hadin bakin soji wurin aikata wannan mummunar aiki

An binne akalla mutum 27 cikin 29 da rahoto ya nuna an kashe a rikicin yankin Nkyie-Doghwro na Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato wanda ya faru a safiyar Litini.

Shugaban Kungiya don Cigaban yankin, mai suna Sunday Abdu ya ce an sassare mutane 27 din har lahira ne a cikin wani aji da a ka yi zargin soji su ka boye su ciki. Ya ce sai daga baya ne aka ga karin wasu gawawwaki 2.

Mutum 27 sun rasa rayukansu a sabon harin da aka kai a jihar Pilato
Mutum 27 sun rasa rayukansu a sabon harin da aka kai a jihar Pilato

Mista Audu ya bayyana takaicin sa kasancewar kashe-kashen bai tsaya ba duk da dokar takaita zirga zirga da gwamnati ta kakaba ranar Juma'a. Ya ce an kashe mutane 41 a yankunan na su a tsawon wata 1.

KARANTA KUMA: Duk da dokar ta baci an sake kai hari tare da kashe mutum 6 a Jihar Filato

A ranar Litini ne mai magana da yawun Shugaban Kasa Buhari wato Garba Shehu, ya ce Buhari ya umurci soji da 'yan sanda da su kawo karhsen wannan rikici kuma su tsayar da kai harin ramuwa da kungiyoyin adawa ke kai wa junan su. Ya kuma mika ta'aziyar sa zuwa Gwamnan Jihar da al'ummar Jihar da kuma iyalai da 'yan uwan wadanda abun ya shafa.

Shugaban Kungiyar CAN na Arewa mai suna Yakubu Pam, ya yi kira da a zauna lafiya. Shi kuwa Kwamanda Soji na kwantar da tarzomar Jos ya ce tuni aka kai sojin da ake zargi zuwa hedkwata don gudanar da bincike.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel