Kungiyar Matan Gwamnonin Jihohin Arewa 19 ta dau alwashin taimakawa Gwamnatin Tarayya

Kungiyar Matan Gwamnonin Jihohin Arewa 19 ta dau alwashin taimakawa Gwamnatin Tarayya

- Kungiyar ta dau wannn alwashin yabo ne bisa ga kokarin da Gwamnatin Tarayya ta yi wurin magance matsalolin Arewa

- Matar Gwamnan Jihar Bauchi ne ta fadi hakan a wani taron Kungiyar da ya gabata

- Ta ce makasudin kungiyar shi ne goyon bayan Uwargidan Shugaban Kasa da kuma Karfafawa Gwamnoni kan aikace-aikacen su

Kungiyar Matan Gwamnonin Arewa, NGWF, ta dau alwashin yabawa Gwamnatin Tarayya bisa kokarin da ta yi wurin magance matsalolin da su ka addabi Arewacin Najeriya.

Hajiya Hadiza Mohammed, matar Gwamnan Jihar Bauchi ita ta dau wannan alwashin yayin bude taron Kungiyar da a ka gudanar jiya a dajin killace namun daji na Yankari ta Jihar Bauchi.

Kungiyar Matan Gwamnonin Jihohin Arewa 19 ta dau alwashin taimakawa Gwamnatin Tarayya
Kungiyar Matan Gwamnonin Jihohin Arewa 19 ta dau alwashin taimakawa Gwamnatin Tarayya

Hajiya Hadiza ta ce matsalolin da Arewa ke fuskanta na rashin lafiya da talauci da rashin aikin yi bai da bambanci da matsalolin sauran yankuna. Don haka ne matan Gwamnonin su ka ga dacewan tallafawa mata da kananan yara.

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga sun yi garkuwa da DPO da wasu mutane 5 a Jihar Neja

Ta ce makasudin wannan kungiya shine goyon bayan Uwargidan Shugaban Kasa da kuma karfafawa Gwamnonin wurin ciyar da Arewa gaba. Za su bada gudummwar su ta kiwon lafiya, ilimin 'ya mace, sana'o'i, tallafawa mata da kuma zaman lafia.

Gwamnan Jihar na Bauchi a na sa jawabin ya yabawa Gwamnatin Buhari bisa ga aikace-aikacen sa. Ya kuma bayyana yadda Gwamnatin Jihar sa ke bayar da magani kyauta ga yara kanana da masu juna biyu da masu shayarwa. Ya kuma bayyana cigaban da Jihar sa ta samu na ilmantar da 'ya'ya mata.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel